Kais Dauda Sallau" />

Akwai Alaka Tsakanin Ta’ammuli Da Kayan Maye Da Matsalar Tsaro A Arewa

Ba shakka matsalar tsaro abu ne wanda ya addabi Arewaci Nijeriya wanda ya hada matsalar ‘yan kungiyan Boko Haram, ‘yan bindiga dadi, fadan kabilanci, masu satar mutane da sauransu. Hakan ya kara kawo ci baya sosai da talauci ga al’ummar Arewa dama Nigeriya gabaki daya.

Matsayar tsoro a Arewacin Nigeriya ya ki ci ya ki cinyewa duk da makuden kudaden da gwamnati ke kashewa a fannin tsoro.
Kuma akasarin masu aikata wadannan miyagun ayyukan matasa ne wanda mafi yawan su ba a cikin hayyacinsu su ke aikatawa wannan miyagun ayyukan ba. Idan mu ka lura dayawa daga cikin masu aikata wadannan ayyukan duk lokacin da a ka kama su sai an same su da miyagun kayan shaye-shaye masu fitar da mutum a cikin hankalinsa irin su kwaya da sauran su.
Haka ko daga maganganun bakin su idan a ka kama su, za ka fahimci cewa akwai abinda su ke sha mai juya mu su tunani, ya kuma cire musu tausayi gaba daya kafin su kai ga aikata danyen aikinsu.
Ya kamata gwamnati su dauki matakai masu tsanani kan masu shiga da kayan maye da masu sayar da shi a kasar nan. Matukar gwamnati ba ta tsaya ta yi yaki da harka da kayan maye a kasar nan ba, gaskiya akwai matsala, domin za a dinga samu tsaiko gurin yaki da matsalar tsaro da a ke yi a Arewacin Nigeriya matukan matasan na samun kayan mayen su na sha.
Allah ya ba mu zaman lafiya a kasarmu.

Exit mobile version