Connect with us

WASANNI

Akwai Banbanci Tsakanin Arsene Wenger Da Unai Emery – In Ji Lacazatte

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar Arsenal, Aledandra Lacazatte ya bayyana cewa duk da cewa burin kowanne mai koyarwa yasamu nasara a wasa amma kuma akwai banbanci tsakanin tsohon kociyan kungiyar Arsene Wenger da sabon kociyan na yanzu Unai Emery.
Emery ya maye gurbin Wenger a matsayin kociyan kungiyar bayan Wenger ya shafe shekaru 22 yana aikin koyar da kungiyar sai dai sabon kociyan yasamu nasara ne kawai a wasa daya cikin wasanni uku da aka buga a gasar firimiya.
A wasan farko kungiyar tasha kashi a hannun zakarun gasar wato Manchester City sannan kuma sukayi rashin nasara a wasan sati na biyu a gidan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea sai dai Arsenal din ta samu nasara a wasa na uku data buga da Westham a gida.
Lacazatte yace “Akwai babban banbanci tsakain masu koyarwar guda biyu duk da cewa burin kowa acikinsu yasamu nasara akan abokan karawarsa amma kuma akwai hanyoyin da kowanne acikinsu yake bi don ganin yasamu nasara”
Yaci gaba da cewa “Wenger ya dade a kungiyar hakan yasa kungiyar ta saba da salon wasansa sannan kuma wasu dayawa daga cikin ‘yan wasan kungiyar sun saba dashi sun saba da salon maganarsa da yadda yakeson kungiyar ta buga wasa”
Lacazatte dai shekara daya kacal yayi da Wenger bayan daya koma kungiyar a kakar wasan data gabata daga kungiyar Lyon akan kudi fam miliyan 52 kuma ya buga wasan da Arsemal din ta samu nasara akan Westham daci 3-1.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: