Akwai Barna A NNPC Duk Da Canjin Gwamnati Da Aka Samu – Bukola Saraki

Har ya zuwa yanzun akwai gagarumar barna da ake tafkawa ta wasoson dukiyar al’umma a Kamfanin Mai na kasa NNPC, duk kuwa da sauyin gwamnati da aka samu shekaru biyu da suka shude. Shugaban Majalisar Dattawa ne, Bukola Saraki, ya yi nu ni da hakan jiya a Abuja. Sarakin ya ce, wannan barnar ta ci gaba da gudana, duk da kokarin da ake yi na tsaftace Kamfanin Man na kasa.

Saraki, wanda jagoran Majalisar, Sanata Ahmad Lawal, ya wakilce shi a wani taron sauraron ra’ayin al’umma kan sake dawo da tallafin Man fetur wanda Kwamitin Majalisar kan albarkatun Man na Fetur ya shirya. Ya bayyana rashin jin dadinsa a kan abin da ya kira da, kumbiya-kumbiyar sake dawo da tallafin Man, ba tare da samun wata yarjewa daga kasafin kudin Majalisar Tarayyar ba.

Shugaban Majalisar ta Dattawa, ya nu na takaicinsa kan, “gwamnati ba ta aiwatar da abin da ya kamata ta aiwatar ba, domin magance matsalar.” A cewarsa, an biya wasu kudade da suka kai Naira Tiriliyon 10, wanda wasu mutane kalilan suka cafka suka kuma amfana da su, su kadai. Ya na cewa, “bincikenmu ya bayyanar da gaskiyar mummunan halin da sassan mu na Mai da kuma Gas ke ciki,: in ji shi.

Saraki, ya kara da cewa, ta bayyana, “Duk da cewar da aka yi an dakatar da bayar da tallafin Mai, amma akwai wasu makudan kudaden da ake biyan wasu da wannan manufan, ta wata hanyar da take kaucewa bincike.”

Ya kuma tabbatar da cewa, Majalisar ta Dattawa, ba za ta gajiya ba, har sai ta tona asirin duk masu aiwatar da wannan barnar, musamman wadanda ke bisa manyan mukamai. Shugaban ya ce, “Wannan Majalisar za ta tona asirin duk wata cuwa-cuwa da ke wakana a wannan tsarin, ba tare da la’akari da ko su waye a cikinta ba. Wannan tsarin da ake bi wanda ya sabawa tsarin mulki, wanda kuma ta barauniyar hanya ne ake aiwatar da shi, ya zama dole mu bincike shi.”

Saraki, sai ya umurci Kwamitin da ya binciki lamarin sosai har ya kai ga tushen badakalar, ya kuma nemo hanyar magance cuwa-cuwar kwata-kwata, a Kamfanin Man,wanda hakan ke kara tsiyata ‘Yan Nijeriya a duk shekara. Sauran tambayoyin da Shugaban Majalisar ya bukaci kwamitin ya gano amsarsu, sun hada da gano hakikanin yawan Man da ‘yan kasuwar Nijeriya ke bukata, da kuma duk wadanda suka sanya hannu a kan kashe kudaden da Majalisan ba ta san da su ba a cikin kasafin kudi.

A wata sabuwa kuma, Kamfanin Man na NNPC, ya yi zargin yana bin gwamnatin Tarayya zunzurutun kudi har Naira bilyan 170.6, na ragowar tallafin Man da gwamnatin ba ta biya ta ba, tun daga watan Janairu na shekarar 2006 zuwa watan Disamban 2015.

Da ya jagoranci manyan ma’aikatan Kamfanin Man, wajen sauraron binciken da Majalisar ke yi kan ta yadda tallafin Man da ya kai har na Naira Tiriliyon 5, daga shekara 2006 zuwa ta 2015, Shugaban Kamfanin, Dakta Maikudi Baru, cewa ya yi, kudin sun kai hakan ne bayan da aka zabge Naira triliyon 4,950,80, da aka biya daga Naira tiriliyon 5,121,40, na tallafin wanda Kamfanin ke bi.

Da yake fayyace lamarin, Shugaban sashen kudi na Kamfanin, Mista Isiaka Abdulrazak, ya bayyana cewa maganan tallafin ta samo asali ne tun daga lokacin da maganan tallafin ta faro zuwa watan Oktoba na shekarar 2003, a lokacin da gwamnati ta umurci kamfanin na NNPC da ya fara sayo tataccen Man daga waje.

Ya kuma bayyana cewa, a karkashin wannan tsarin na tallafi, Kamfanin na NNPC, da sauran dillalan da ke shigo da tataccen Man, suna da daman neman a biya su duk kudaden da suka cika daga sashen kamfanin wanda ake kira da PPPRA,  Abdurrazak, ya ce, sai dai kuma ba kamar sauran dillalan da ke shigo da Man ba, su ba a biyansu da tsabar kudi, sai dai a zame kawai daga kudaden da kamfanin ke biyan gwamnatin ta Tarayya a duk wata.

“A takaice dai, Kamfanin na NNPC, ya gabatar da cewa, sama da Naira Triliyon 5.1 ne sashen na PPPRA ya sanya hannu a biya kamfanin na NNPC a matsayin tallafin da ya biyo, daga cikin wadannan kudin, har yanzun kamfanin na NNPC, yana bin Naira bilyan 170.6.

Sai kamfanin ya nemi kwamitin na Majalisar ta Dattawa, da ya taimaka a biya kamfanin sauran kudaden da ya biyo, domin tabbatar da ci gaban kamfanin.

 

Exit mobile version