Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Akwai Buƙatar A Farfaɗo Da Mutuncin Kaduna -Alhaji Uba Lamuni

by Tayo Adelaja
October 16, 2017
in LABARAI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

An shawarci gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufai da ya haɗa hannu da gwamnonin arewa goma sha tara,su tsara yadda za su dawo da ɗaukakar da garin Kaduna, kamar yadda garin ya ke a lokacin Sa-Ahmadu Bello da ayarinsa.

samndaads

Wannan shawara ta fito ne daga wani shugaban al’umma kuma mai tsokaci kan al’amurran yau da kullum mai suna Alhaji Uba Zariya,wanda aka fi sani da Uba Lmuni.

Alhaji Uba Lamuni ya ci gaba da cewar,duk wanda ya san garin Kaduna,kafin turawa su kasance a Nijeriya,ya san garin Kaduna,gari ne da duk wani ɗan Nijeriya ke tinƙaho da garin,musamman a ɓangaren masana’antu da kuma yadda aka samar da cibiyoyin ilimim a garin Kadunan.

A nan ne fitaccen mai tsokaci da al’amurran yau da kullun,y ace da tafiya-ta-yi –tafiya sai matsayin da garin Kaduna ke da shi ya dunga raguwa daga lokaci zuwa lokaci,wannan kuma ya faru ne,a cewarsa,a dalilin rashin kishin wasu magadan Gamji,yadda suka yi sakaci amanar da Sa-Ahmadu Bello ya danƙa ma su a waɗancan shekaru da suka gabata.

Alhaji Lamuni y aba da misali da garin Fatakwal da jinsin inyamurai suka bunƙasa garin da duk abin da za a ce gari ya mallak,da ya shafi kasuwanci da da-dai sauran abubuwa ma su yawan gaske.Ya ci gaba da cewar,kishin jinsin yarbawa ne ya sa garin Ikko ya sami ɗaukaka a ɓangaren kasuwanci da samar da kamfanoni ma su yawa da suke samar da ayyukan yi ga matasan waɗancan yankuna

Duk ci gaban da aka furta an samu a manyan garuruwa biyu da aka ambata,da arzikin arewa aka bunƙasa su,wato da Auduga da kuma Gyaɗa da al’ummar arewa suka samar da jiɓing goshi,daga baya,in ji shi,sai ake zunɗen ‘yan arewa an ace ma su ci-ma zaune da dai sauran maganganu marasa kyau.

Alhaji Uba Lmuni ya tabbatar da cewar,ya san in har gwamna Malam Nasir El-rufaiya jajirce,kamar yadda ya tashi tsaye a yau wajen ciyar da jihar Kaduna gaba.Kuma,ya ci gaba da cewar,in har gwamna El-rufaiya yi niyyar farfaɗo da garin Kaduna ta haɗa hannu da gwamnonin arewa,abu ne mai sauƙi a wajensa.

Aƙarshen ganawarsa da wakilinmu,Alhaji Uba Zariya,wato Uba Lamuni,yay i kira ga ɗaukacin ma su faɗa a ji a jihar Kaduna su fara tunanin ire-iren gudunmwar da ya dace su bayar ta yadda za a sami damar farfaɗo da mutuncin garin Kaduna a ɗan lokaci kaɗan.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Za A Fara Nuna Fim Ɗin Tarihin Shehu Ɗan Fodiyo A Bauchi

Next Post

’Yan Bindiga Sun Hallaka Jami’an NDLEA A Kogi

RelatedPosts

Hadiza Usman

Hadiza Bala Usman Ta Yi Ta’aziya Ga Iyalan Marigayi Dikko Inde

by Sulaiman Ibrahim
1 hour ago
0

Daga Abdullahi Sheme A ranar juma'ar da ta gabatane shugabar...

Masana Sun Yaba Wa Shugaba Buhari Kan Sake Nada Hadiza Bala Usman Shugabar NPA

Masana Sun Yaba Wa Shugaba Buhari Kan Sake Nada Hadiza Bala Usman Shugabar NPA

by Sulaiman Ibrahim
1 hour ago
0

Daga Bello Hamza, Abuja Masana da masu ruwa da tsaki...

An Sako Daliban Da Aka Sace A Zamfara

An Sako Daliban Da Aka Sace A Zamfara

by Muhammad
2 hours ago
0

Rahotanni daga jihar Zamfara sun tabbatar da cewa an ceto...

Next Post

’Yan Bindiga Sun Hallaka Jami’an NDLEA A Kogi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version