Daga Mustapha Ibrahim,
Hon. Suleman Dalibi ’Yargaya, Sardaunan Matasa, ya bayyana cewa akwai bukatar ba matasa dama mai yawa a gwamnatin kano karkashin shugabancin Dr Abdullahi Umar Ganduje duk da yake cewa Gwamnatin Kano tayi na mujin kokari da kuma ajiye tarihi ganin yadda a zamanin Dr.Abdullahi umar Ganduje ne aka kirkiri ma’aikatar matasa kuma aka matashi mai kanan shekaru shugabancin a matsayin kwamshin kuma matashi mai jinni ajiki wannan abu a yabawa Gwamnatin kano ne ga kuma zaben shugabanin kananan hukumumi kano 44 da akayi a watan day a gabata shima gwamnana kano ya ba matasa dama wanda mafiya yawansu matasa ne, sai dai kuma muna da bukatar karin guraban matasa masu yawa a Gwamnatin Kano da ta kasa baki daya.
Sardaunan matasa ya bayana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke kano ya ce bisa laakari da yadda matasa suke bada gudinmawa akon wane irin zabe to akwai bukatar kara basu dama a matakain a gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari duk da yake itama anba matasa dama musammam idan kai la
akari da ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami ga kuma sabon shugaban hukumar hana al`mundahana ta EFCC da aka ba Bawa suma duk matasa ne amma dai mu matasa muna bukatar karin gurabai maasu yawa a Gwamnatin Kano da ta Najeriya.
Har ila yau Hon Suleman dalibi yar Gaya yace tun da Najeriya ta samu yanci a 1960 zakaga wadanda sukayi raawar gani a tarihi irinsu marigayi Muartala Muhammad tsowan shugaban kasa irinsu Gawan irinsu Buhari day a yi ministan man fetir kuma ya yi Gwamnan mai Dugori duk yana matashi ga kuma irinsu tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Baban Gaida da dai sauransu.