Bello Hamza" />

Akwai Bukatar Dorawa Kamfanonin Sadarwa Harajin Kula Da Lafiyar ‘Yan Nijeriya

An shawarci gwamnatin Nijeriya ta dora harajin kwabo daya  a kan duk kiran da aka yi daga kuwanne kamfanin sadarwa dake harkar a kasar nan don a sanya kudaden wajen kula da lafiyar ‘yan Nijeriya.

Wata gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu da kuma wasu kungiyoyin masana a bangaren kula da lafiyar yara suka bayar da wannna shawarar a ranar Litinin a garin Abuja, sun bayar da shawarar be a yayin bikin ranar lafiyar jama’a ta Duniya ‘International Unibersal Health Coberage (IUHC) Day’.

Ana bikin ranar kula da lafiya jama’a ta duniya ce a kowacce ranar 12 ga watan Disamba, taken bikin wannnan sherara shi ne, “Unite for Unibersal Health Coberage: Now is the time for collectibe action.”

A gudanar da taron manema labaran ne kwana daya bayan an kammala taron kara wa juna sanin ne da kungiyoyin suka shirya don fadakar da jama’a irin cututukan da ake dauka ta hanyar amfani da waya.

UHC na nufin tsarin da zai ba dukkan dan kasa damar samun kulawa da kyakyawar magani a dukkan inda yake a fadin tarayyar kasar nan, ba tare da mutum ya samu mastala ba sakamakon rashin kudi da makamantansu.

A kan sabon kiran da kungiyoyin suke yi a wannna lokacin, sun bayyana cewa, suna bukatar gwamnatin tarayya ne ta dora  harajin kwabo daya a kan dukkan kiran wayar salula da ake yi a kasar nan don mayar da kudaden cikin bangaren samar da lafiya ga ‘yan Nijeriya.

Da yake jawabi a wurin taron, mataimakin shugaban kungiyar likitoici masu kula da cututtukan mata da  da yara ‘Society of Gynecology and Obstetrics (SOGON), Habib Sadauki, ya yi kira ne na a hada hannu don fuskantar bukatar samar da cikakken kiwon lafiya ga al’ummar Nijerya na da matukar mahimammanci, don haka ake a dukkan sauran kasashen duniya, kuma dole a buda don neman hanyoyin samun kudaden da za a gudanar da ayyukan da ya kamata, abin da yasa ya nuna goyon bayansa a kan kiran a nemi kudade daga hannun kamfanonin sadarwa irinsu MTN da ETISALAT don irin cutuwar da mutane ke funskanta ta hanyar amfani da wayoyin salula, ana fuskantar cuta tun daga bangaren kunne da kwakwalwa da kuma shiga cikin matsalar damuwa da wasu mutane ke shiga sakamakon amfami da wayar sadarwa ta salula.

Mista Sadauki ya ce, bukatar a dora harajin kwabo daya a kan kowannen kiran da aka yi a Nijeriya yana da alfanu, ya kuma ce tuni wani dan majalisa a majalisar kasa ya gabatar da daftarin dokar ga majalisar don ta amince ta zama doka a Nijeriya, ya ce, a halin yanzu dokan ya wuce mataki na biyu, amma an samu matsalar rashin ci gaba da daftarin dokar ne saboda dan majalsiar da ya yi kokarin gabatar da dokar bai samu dawowa majalisa ba don ya fadi zabe.

“Rashin ci gaban daftarin dokar saboda rashin dawowar dan majasiar bai kamata a ce dokar ta kin ci gaba da tafiya ba, ko ba komai kusan dukkan ‘yan Nijeriya na amfani da wayar salula, don kuwa hukumar kula da harkokin sadarwa da kasa ‘Nigerian Communications Commission’ ta bayyana cewa, a kwai layukan wayar salula a hannu ‘yan Nijeriya da ya kai Miliyan 162. 3. Saboda haka samun kudade daga wannnna bangaren zai yi matukar taimaka wa wajen cinmma burin da UHC ta sa a gaba na kula da lafiyar al’ummar kasa,” ini shi.

Ya kuma kara da cewa, yawancin mutanen da ba su da ikon samu cikakken kulawa na magani yadda ya kamata su ne wadanda basa aikin gwamnati ko na kamfanoni masu zaman kansu.

“A kan haka ne muke da kyakyawar zaton kudaden da za a samu a wannnan banagaren zai yi matukar taimaka wa wajen bayar da tallafin kiwon lafiya ga dimbin jama’ar Nijeriya. Ya kamata ‘yan Nijeria su hada hannun don cimma wannna nasarar,” inji shi.

A nata jawabin, shugabar kungiyar ‘Women in Media (WIM),’ Halima Ben-Umar, ta bukaci hada kai don cimma wannna bukatar na dora harajin kwabo daya a kan dukkan kiran da za a yi a kasar, musamman ganin irin cututtkan dake tattare da amfani da wayar salula suna nan za su ci gaba da bayyana a shekaru masu zuwa, dole a samar da kudade nayin bincike da skuma samar da kwararrun da za su tallafa wajen samar da cikakken kulawa a lokacin da cututtukan suka bayyana.

Ta kuma yi alkawarin amfani da kungiyarta a wajen fadakar da jama’a a kan illolin dake tattare da yawan amfani da waya sallula, musamman yadda mata ke sanya wayar a cikin rigar mamansu, bincike ya nuna cewa, a na yawan samu kamuwa da kandar nono ta wannna hanyar, haka kuma maza masu sa wayar a cikin aljihu kusa da al’aurarsu yana iya haifar musu da matsala a mazakutansu hakan kuma na iya hana su haihuwa.

Exit mobile version