Ammar Muhammad" />

Akwai Bukatar Gwamnonin Arewa Su Yi Yaki Da Talauci-Dangote

Shahararren dan kasuwarnan a nahiyar Afirika ma baki daya, kuma shugaban rukunin Kamfanin Dangote, wato Aliko Dangote a jiya Laraba ya bayyana damuwarsa na yadda ake samun karuwar talauci a arewacin Nijeriya, ya ce akwai bukatar gwamnoni da su tashi tsaye wajen magance wannan matsalar.

Dangote ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa a matsayin babban mai gabatar da kasida a taron tattalin arziki da zuba jari a jihar Kaduna a karo na 4 wato KADInvest 4.0 a takaice.

Dangote ya ce; kashi 60 na mutanen Arewa suna rayuwa ne cikin matsanancin talauci, ya ce; sam wannan ba abin a amince da shi ba ne a ce yankin da suke da kasar noma amma suna fama da irin wannan talaucin.

Dangote ya shawarci Gwamnonin yankin Arewa da su mike su kuma tashi tsaye domin fitar da yankin daga wannan kangin na matsalar tattalin arziki da ake fama da shi.

Ya ce; yanzu lokaci ne da Arewa za su tashi tsaye su mike su baiwa bangaren noma muhimmanci ta hanyar sarrafa kayan noman. Ya ce; bai kamata irin wadannan yanki masu arzikin kasar noma ya zama suna fama da talauci ba.

Ya ce; yana fatan dukkanin gwamnonin Arewa guda 19, za su tashi tsaye domin koyi da gwamnatin jihar Kaduna. Ya ce; a yadda ya kallo, idan har aka baiwa bangaren noma muhimmanci, nan da shekaru 10 masu zuwa, bangaren noman zai rika samar da harajin da sai ya fi bangaren mai.

Exit mobile version