Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Akwai Bukatar Hada Aikin Yaki Da COVID-19 Da Na Farfado Da Tattalin Arziki Da Zamantakewar Duniya

Published

on

Sanin kowa ne barkewar annobar COVID-19 ta yi gagarumin tasiri mai muni ba ga tsarin kiwon lafiya kadai ba, domin ta fada zuwa bangaren tattalin arziki da dukkan harkokin kasuwanci da na rayuwar yau da kullum, inda har take barazanar kara jefa mutane cikin mawuyacin hali. Watanni kimanin 6 bayan barkewarta, har yanzu tana nan tana cin karenta babu babbaka, wanda ba haka aka yi zato ba.

Yayin taro na 22 na kasar Sin da shugabannin Tarayyar Turai, Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce dole ne Sin da Tarayyar Turai, su hada hannu wajen samar da cikakkiyar yarjejeniya mai cike da adalci, da za ta habaka harkokin zuba jari, da nufin ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya. Ya kuma jaddada bukatar inganta hadin gwiwar banagrorin biyu a matsayinsu na masu karfin tattalin arziki a duniya, domin farfado da tattalin arzikin duniya da bunkasa cinikayya cikin ’yanci da kuma huldar kasa da kasa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Darakta Janar na hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ke cewa, babu zabi tsakanin rayuwa ko kuma zaman rayuwar al’umma. Ya ce kasashen duniya za su iya hada ayyukan inganta bangarorin biyu. Ya ce dukkan kasashen duniya na cikin wani yanayi na tsaka mai wuya game da batun baiwa jama’arsu kariya, a hannu guda kuma, rage tasirin annobar kan zaman rayuwa da tattalin arziki.
Abu mai matukar muhimmanci a wannan lokaci shi ne daidaita matakan yaki da annobar da na farfado da tattalin arziki da zamantakewa. Wadannan bangarori biyu, abubuwa ne da suka zama tilas su tafi tare. Yayin da ake yaki da annobar, bai kamata kuma a dauke ido daga kokarin raya tattalin arziki ba, domin yin haka ka iya haifar da mummunan illar da ta zarce ta annobar.
Tasirin annobar a kan tattalin arziki ya durkusar da harkoki da dama tare da haifar da koma baya ga kasuwanni mafi juriya da kuma barazana ga ci gaban kasashe da na duniya baki daya. Tuni alkaluman tattalin arzikin duniya suka girgiza saboda annobar. Bangaren bada hidima, ciki har da bangaren zirga-zirgar jiragen sama, tafiye-tafiye da yawon bude ido, su suka fi shiga mawuyacin hali. Harkokin kasuwanci a kasashe da dama musamman kasashe masu tasowa ya tsaya cik. Kananan da matsakaitan sana’o’i sun fi jin jiki a wannan lokaci, lamarin da ya kai ga raba dubban mutane da ayyukan da suka dogara da su, wanda kuma zai kara jefa su cikin kuncin rayuwa.
Kungiyar kawancen tattalin arziki da ci gaba, ta yi hasashen cewa, wasu kasashe za su shafe shekaru masu zuwa suna ci gaba da yaki da tasirin da annobar COVID-19 ta haifar.
Shawo kan matsalolin da annobar ta haifar ko take ci gaba da haifarwa, sun dogara ne da irin yadda aka kara tashi tsaye wajen yaki da ita da managartan matakan da gwamantoci za su dauka da yadda mutane ke aiwatar da matakan kandagarki da kuma irin tallafin da hukumomin raya kasa za su bayar wajen tunkarar matsalar. Haka zalika, samar da magunguna da allurar riga kafi, za su taimaka gaya wajen shawo kanta.
Ya kamata kasashen duniya su yi koyi da kasar Sin. Duk da cewa tana fuskantar annobar, hakan bai hana ta tashi tsaye wajen farfado da harkokin tattalin arziki da zaman takewa ba. Tun bayan bullar cutar, ta jajirce ta kuma himmantu wajen hada ayyukan yaki da annobar, da kuma farfado da harkoki, kana take ta kira da a hada hannu wajen farfado da harkokin tattalin arziki a duniya.
Jazaman ne sauran gwamnatocin kasashe su tashi tsaye wajen ganin sun hada ayyukan domin abubuwa ne biyu dake tafiya kafada da kafada. Yaki da annobar na bukatar jajircewa da kaifin basira hangen nesa irin na kasar Sin. Yayin da ake daukar matakan dakile ta, a daya hannun sai a yi la’akari da matakan farfado da harkokin tattalin arziki, da lalubo sabbin dabarun samar da ci gaba.
Hakika wannan annoba ta zama darasi ga al’ummomin duniya. Bisa la’akari da yadda ta mamayi duniya gaba daya ba zato ba tsammani, ya kamata a sake nazartar dabarun raya tattalin arziki da zaman takewa domin kaucewa sake aukuwa irin wannan yanayi a gaba. Kamata ya yi a kara gina wani tubali mai kwari na raya harkokin tattalin arziki, ta yadda zai kasance mai juriya yayin da ake fuskantar barazana mai tsanani. (Marubuciya: Fa’iza Mustapha)
Advertisement

labarai