An yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dinga samar da ingantattun bayanai ga masana’antun da ke sarrafa Kwakwar Manja a kasar nan, inda kungiyar kuma ta yi nuni da cewa, sai dai, gwamnatun ta Gaza wajen tabbatar da hakan.
kungiyar ta kasa (NPPAN) ce ta bayyana hakan, inda ta kara da cewa, raahin yin hakan ga masana’antun har yanzu babbar matsala ce, inda kuma yi kira ga gwamnati da ta samar da ingantattun bayanai ga masana’antar don kirkirar ingantaccen tsari da aiwatar da shirye-shirye yadda ya kamata don samar da mai a kasar, inda ya yi nuni da cewa, Kwakwar Manja na iya samar da mai fiye da kowane irin da a ka shuka.
A cewar kungiyar, ana amfani da kusan kashi 90 na Manjan a cikin samar da abinci, yayin da ragowar kashi 10 kuma masana’antar ba abinci take amfani da su ba ‘yan wasan masana’antu.
kungiyar, abubuwan abinci kamar, kayan lambu da sauran su, ana kuma yin amfani da Kwakwar Manjan wajen sarrafa wasu abubuwa, kamar sabulun wanka, har ma ana yin kwaskwarima daga Kwakwar ta Manja.
A wata sabuwa kuwa, Babban Bankin Nijeriya CBN ya zabi kungiyar don ta amfana a karshin shirin bayar ta tallafin aikin noma na Anchor Borrowers.
A hirarsa da manema.labarai shugaban ya ci gaba da cewa, Babban Bankin Nijeriya CBN, ya zabi kungiyar don ta noma Kwakwar Manja ta musamman, inda ya kara da cewa, a yanzu kungiyar tana kan tattaunawa da Babban Bankin Nijeriya CBN kan yadda za’a tunkari aikin.
A cewar kungiyar Manoman Kwakwar Manja ta kasa fasahar da ake da ita a kasar nan, ta karu matuka wajen sarrafa Kwakwar Manja ta musamman a cikin kasar, inda kngiyar Manoman Kwakwar Manja ta kasa ta yi amannar cewa, shirin zai taimaka matuka wajen kara daga tattalin arzikin kasar nan, inda ya kara da cewa, Babban Bankin Nijeriya CBN a yanzu, ne ya ke yin aiki da Manoman dake a cikin kasar nan wadada kuma suke samar da kimanin kashi 80 bisa dari na Manjan da ake yin amfani dashi a cikin kasar nan, inda ya sanar da cewa, akwai matukar wahala wajen iya tafiyar da Manoman Kwakwar Manja dake a cikin karkara.
Har ila yau, wasu manoman Kashu da kuma masu fitar dashi daga kasar nan zuwa kasuwannin duniya, su na shirin tara kudaden shiga da suka kai dala miliyan 350 a shekarar 2020 ta hanyar fitar da shi zuwa waje.
Muna Bukatar Takin Zamani –Manoman Rogo A Kwara
Manoman Rogo a jihar Kwara sun yi kira ga gwamnatin...