Akwai Bukatar Kafa Mahukuntan Hukumar Sayar Da Hannun Jari Ta Kasa – Ambrose

Babban Jami’i na kamfanin InbestData, Mista Ambrose Omordion, ya shawaci gwamnatin tarayya ta kafa mahukuntan Hukumar sayen hannun jari ta kasa.

Mista Ambrose Omordionya bayar da shawar ce a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa a lokacin da yake Magana akan abinda suke tsimayi gdaga gun gwamnatin tarayyar.

kamfanin dillancin labarai na kasa, ya ruwaito Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rusa mahukuntan hukumar a ranar 16 ga watan Yulin 2015, inda daga baya, ya kafa kwamiti mai mutane takwas da tsohon Skataren Gwamnatin Tarayya yake Mista Babachir Lawal ya jagoranta.

Omordion ya sanar da cewar, gazawar gwamnatin na kafa mahukuntyan hukumar sama da shekaru uku da suka wuce, yana sahafar ayyukan hukumar da kuma karyawa masu zuba jari a kasuwar gwiwa.

Ya yi nuni da cewar, akwai bukatar a karfafa hukumar ta hanyar sanya mata daraktoci don ciyar da kasuwar gaba.

Omordion ya kara da cewar, akwai bukatar daukacin matakan gwamnati su mayar da hankali wajen ciyar da tattalin arzikin kasar nan don kara samar da ci gaba ganin cewar, an kammala zabubbukan 2019.

Ya kuma yi kira ga gwamnati data kara mayar da hankali a fannin fasaha, musamnna don kara ciyar da tattalin arzikin kasar nan da rage yawan marasa aikin yi.

Omordion ya kuma bayar da shawara akan inganta kasafin kudi da tsara shi don a tabbatar da amincewa da kasafin a cikin  lokacin daga Janiru zuwa Fabirairu na ko wacce shekara.

Ya kuma shawarci gwamnatin ta ta fara wayar da kan yan kasa akan tsare-tsaren tattalin arzikin ksar nan, musamnna don ciyar da matsakaitan sana’oi gaba.

A karshe Omordion ya ce, ana sa ran kasuywar zata fara da kafar dama bayan kammala zabububbukan da aka gudanar a Nijeriya.

Exit mobile version