Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
An bai wa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya shawarar ta nemi goyon baya da tallafi daga sojojin haya a kasashen waje, domin bayar da damar yakar ’yan ta’adda da sauran matsalolin tsaro da suke addabar kasar bisa lura da zahirin zancen cewa, dakarun sojin Nijeriya ba su da karfin da za su iya yaki da ’yan ta’addar da suke cin karensu babu-babbaka a fadin kasar.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a lokacin da yake bude taron ganawar gwamnonin Arewa maso Gabas Karo na Hudu, wanda ya gudana a gidan gwamnatin Jihar Bauchi a jiya, yana mai cewa, babu bukatar bata lokaci wajen yaki da matsalar tsaro.
Har-ila-yau, ya kuma bukaci da a gaggauta maida dukkanin makarantun kwana da suke Arewa zuwa makarantun jeka-ka-dawo bisa karancin jami’an tsaron da ake da su da za su iya tsare su, domin kare afkuwar garkuwa da mutanen da ake yi, musamman a jihohin Katsina, Neja, Zamfara da sauran yankuna.
Zulum, wanda kuma shine shugaban kungiyar ta NEGF, ya nuna cewa, matsalar tsaro ta addabi jiharsa ta Borno sosai, inda a yanzu haka wasu sassan jihar ba su da wutar lantarki sakamakon lalata layukan lantarkin da aka yi sakamakon matsalolin ‘yan ta’adda da suka haifar.
Gwamnan ya nemi gwamnatoci a dukkanin matakai da su tashi tsaye wajen shawo kan matsalolin tsaro musamman a shiyyar arewa maso gabas lura da cewa ‘yan ta’adda suna cigaba da cin karensu babu babbaka har zuwa yanzu.
A cewarsa, sakamakon yawaitar kisan mutane da ‘yan ta’adda ke yi, akwai bukatar a sake fito da wasu sabbin matakan yaki da matsalar tsaron don kare rayukan jama’a a sassan kasar nan.
Ya ce, “Akwai bukatar gwamnati ta nemi agaji daga kasashen makwafta irin su Jamhuriyyar Chadi, Kamaru da kasar Nijar domin daukan matakin hadaka don neman dakile matsalar tsaron,”
“Don haka gwamnatin tarayya ta duba yiyuwar shigo da sojojin haya domin neman shawo kan matsalar tsaro. Don tabbatar da shawo kan matsalar tsaro, muna da bukatar hada karfi da karfe da kuma neman tallafi daga waje,” a cewarsa.
A cewarsa, a bangarensu za su yi iyaka kokarinsu wajen ganin sun taimaka wa sojoji da kayan aiki da kudade domin ba su kwarin guiwar cigaba da yakar matsalar tsaro a kasar nan.
Wakazalika, gwamnan na Borno ya shawarci sabbin hukumomin tsaro da su fiddo da sabbin tsare-tsare da dabarun yaki da matsalar tsaro musamman a shiyyar arewa maso gabas.
Tun da farko a jawabinsa na lale, Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, wanda shine mai masaukin baki, ya shaida cewar akwai bukatar tashi tsaye wajen yaki da ’yan ta’adda da ta’addanci, tare da yin kukan kura gaba daya don yin kwaf daya wa ‘yan ta’adda.
“Yayin da aka yi kukan kurar yaki da ‘yan ta’addar nan, ba za su samu damar da za su sake hada kungiya balle su cigaba da aika-aikarsu. Don haka zaman lafiya zai dawo daga shiyyar,” inji shi.
Gwamna Bala Muhammad ya kuma ce yaki da matsalar tsaron nan dukkaninsu ya shafa a shiyyar, inda ya nuna cewa a yayin da Maiduguri ke tsaka mai wuya kan aikace-aikacen ‘yan ta’adda, su kansu ba su tsira ba. Don haka ne ya nemi cewa dole ne fa hukumomin tsaro su sake azama domin ganin an kawo karshen ‘yan ta’addan nan.
“Ba zai yiwu mana mu zauna kawai muna kallon ‘yan ta’adda na addabarmu ba, dole ne mu tashi tsaye da karfinmu mu yake su, dole ne mu tabbatar da kare shiyyarmu daga hannun tsirarun ‘yan ta’adda. Dole ne mu yi dukkanin mai yiyuwa domin kare jama’anmu daga ‘yan ta’adda.”
Gwamnan, wanda ya nuna cewa jihar Bauchi jiha ce mai cin gajiyar zaman lafiya sosai, amma duk da hakan halin matsalar tsaro da sauran jihohin da suke makwaftansu ke ciki abun na damun su, don haka dole ne su zauna domin duba yadda za su kawo karshen matsalar.
Wakilin LEADERSHIP A YAU ya nakalto cewa, gwamnonin za su yi tattauna ta musamman a tsakaninsu, domin fito da shawarori da matsayar da za su dauka kan lamuran da suka addabi shiyyar bakidaya.
Gwamnonin shiyyar ta Arewa maso Gabas sun hada Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad; Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya; Gwamnan Jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri; Gwamnan Jihar Tabara, Darius Ishaku, da kuma Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin shiyyar, sai kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.