Idris Aliyu Daudawa" />

Akwai Bukatar Sanin Kididdigar Kashe Kudade A Bangaren Lafiya – Likita

Daya daga cikin manyan bakin da suka tattauna game da matsalolin dake hana samun ci gaba a fannin kiwon lafiyar kasar Nijeriya Dokta Dale Ogunbayo ya yi kira ga mutane da su rika yin tambayoyi dangane da yadda ake kashe kudaden da gwamnati ke ware wa bangaren kiwon lafiya.

Ogunbayo bayyana hakan ne lokakacin da yake hira da kafar sadarwa ta PREMIUM TIMES a wani taron tattauna matsalolin dake cima banagaren lafiya tuwo a kwarya a Nijeriya. wa fannin kiwon lafiya tuwo a kwarya. Shi dai wannan taron an gudanar da shi ne a a ranakun 15 da kuma 16 na watan Oktoba a Otel Nicon Ludury dake Abuja.

An gayyaci masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon lafiya domin ganin yadda talakawan Nijeriya zasu iya samun kiwon lafiya na gari a cikn kudade kalilan.

Ogunbyo ya kara da cewar za a samu nasara ta hakan ne kawai idan mutane suna bin diddikin yadda ake kashe su kudaden, maimakon a barsu a hannun mahukunta suna yin abin da suka ga dama da kudaden jama’a.

“A yanzu haka su kudaden da gwamnati ke ware wa bangaren kiwon lafiya basu isar shi fannin, bayanan kuma duk shekara gwamnati na kara rage wakannan kudaden maimakon ma a kara yawan su.

Daga karshe ya yi kira da gwamnati da ta maida hankali wajen kara ware wa bangaren kiwon lafiyan kudade masu tsoka.

Exit mobile version