Firaministan Sin Li Qiang ya bayyana a yau Laraba cewa, a matsayinsu na muhimman membobin kasashe masu tasowa, ya kamata Sin da Masar su karfafa hadin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare, domin kare muradunsu na bai daya.
Li Qiang ya bayyana haka ne bayan isarsa birnin Alkahira, a ziyarar aiki da yake yi a kasar bisa gayyatar takwaransa na Masar din, Mostafa Kamal Madbouly.
Firaministan Masar da sauran manyan jami’an gwamnatin kasar ne suka tarbi Li Qiang tare da shirya biki domin yi masa maraba. Kafin isarsa, Li Qiang ya halarci taron kungiyar BRICS karo na 17 a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)