Ministan sufuri, Rotimi Amaech ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya za ta kammala kwangilar yin titin jirgin kasa tun daga Ibadan har zuwa Kano da zarar gwamnatin kasar China ta bayar da bashin dala 5.3. domin kammala dukkan titin jiragen kasa ne ya sa gwamnatin Nijeria ta nemo basi daga gwamnatin kasar China. Ministan ya bayyana cewa, sauran masu zuba jari wadanda suke sha’awar taimaka wa Nijeriya wajen ci gaba za su yi hakan daga baya.
Da ake tattaunawa a wani shiri na gidan talabijin NTA da ke garin Abuja, mahukunta sun bayyana cewa, tuni gwamnatin Nijeriya ta amince da bayar da kwangilar hanyar jirgin kasan.
“Muna ciran gwamnatin kasar China ta amince da bayar da bashin dala biliyan 5.3 domin kammala kwangilar titin jirgin kasa tun daga Ibadan har zuwa Kano. Gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar tun a shekarar da ta gabata.
“A duk lokacin da gwamnatin tarayya ta samu nasarar samun bashin dala biliyan 5.3 daga gwamnatin kasar China, to za a kammala kwangilar titin jirgin daga Ibadan zuwa Kano.
Mista Amaechi ya bayyana cewa, titin jirgi tsakanin Ibadan zuwa Kano zai hade yankuna guda shiga wadanda suka hada da Kaduna zuwa Kano da Abuja da Minna da Ilorin da Oshogbo da Ibadan, inda za a dunga kai kayan jirgi tun daga Legas zuwa Kano.
Ya kara da cewa, idan aka samu nasarar kammala aikin, za a samu raguwar hadararruka, sannan za a dunga kai kayayyakin a jirgin kasa tun daga Legas har zuwa Ibadan.
Ya ce, idan aka samu nasarar kammala titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano, to za a dunga safarar kayayyaki tun daga Legas har zuwa Kano ta jirgin kasa ba tare da wata matsala ba.
Ya ci gaba da cewa, ya kamata ‘yan Nijeriya su kara hakuri an kusa share musu hawayansu a bangaren sufuri ta jiragen kasa. Misa Amaechi ya ci gaba da cewa, ma’aikatan kude ce take bayar da kudaden ayyukan jiragen kasa ba ma’aikatan sufuri ba. Ya kara da cewa, shugaban kasa ya amince da amso bashin kudaden domin a samu nasarar gudanar da ayyukan yadda ya kamata.