Daga Abdullahi Sheme
Majalisar dokoki da ta zartarwa a jihar Katsina a kwai kyakkyawar alaka da fahimtar juna wajen yi wa al’ummar jihar aiki wannan tabbacin. Hakan ya fito ne daga baki xan Majalisar dokoki ta jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Funtuwa a zauren Majalisar, Alhaji Abubakar Muhammad Total jim kadan da kammala taron masu fada a ji na jam’iyyar APC na karamar hukumar mulki ta Funtuwa dake jihar Katina a lokacin da yake zantawa da manema labarai, Alhaj Abubakar yaci gaba da cewar an kira taron masu ruwa da tsaki na karamar hukumar daga ko wacce mazaba guda 11 dake a karamar hukumar Funtuwa da sauran jiga jigan ya yan jam’iyyar APC na jihar Katsina ‘yan asalin karamar hukumar akwai maigirma kwamishinan Albarkatun na jiahar Alhaji Musa Adamu Dankafin Katsina da shugaban jami’yyar na karamar hukumar da da Babban Sakatare a maikatar jihar Katsina Alhaji Hassan Musa Funtuwa da Alhaji Rabiu Adamu da dai sauran manya manyan ya yan jam’iyyar wajen wayar da kan ‘ya’yan jami’yyar domin sanin mahimmancin yin katina zama xan jami’yya, ya ci gaba da cewar babu shakka taron ya samu halatar kowa da kowa waxanda a ka gayyato ya ci gaba da cewar yin katin zama dan jam’iyya yana da mahimmancin sosai sai da katin kake cikakken xan jam’iyya sannan da shine mutum zai iya tsayama jam’iyyarshi Kuma Sai da katin ne zaka iya yin zaben fidda gwani na jam’iyyar yace a kwai kwamitoci guda biyu da za a kafa daya na mazabar kansila dana a kwatuna bayan kwamitin na karamar hukuma da Kuma mutanen da za a ba horo na musamman don gudanar da aikin da ya juya wajen alakar dake tsakaninsu su yan majalisar dokokin da majalisar zartarwa ta jihar Katsina yace suna zaman lafiya Kuma suna aiki kafada da kafada don ciyar da jihar gaba ba shakka kwalliya ta biya kuxin sabulu idan ka dubi yadda Gwamnatin maigirma Dallatun Katsina ta gabatar da manyan ayyuka a faxin jihar Katsina musamman a nan mazabata ta Funtuwa an yi manyan ayyuka kamar irinsu Gina kasuwa hade da tashar mota ta zamani hanyoyi asibitoci manyan magudanun ruwa wutar lantarki makarantu kwalbatoci abinda Gwamnatin Alhaji Aminu masari tayi a jihar Katsina da karamar hukumar Funtuwa Basu kirguwa tunda a kasami jihar Katsina a shekar 1987 ba a Sami Gwamnan dake sauraren dan majalisarshi ba kamar matawallen Hausa Alhaji Aminu Bello indai kaje mashi da maganar aikin jama a ne Wanda ya shafi mazabarka zai tabbatar da angudar dashi a wannan mazabar gashi mutum ne mai tausayi kuma dattijo yace sannan su a majalisar dokoki ta jihar suna zaune lafiya da junansu uwa daya uba daya suke don suna mutunta junansu dukkansu ya yan jam’iyyar APC ne A lokacin da Shima kwamishinan Albarkatun ruwa na jihar Katsina Alhaji Musa Adamu Dankafin Katsina ya yabama uwar jam’iyyar ta kasa don yin katin zama xan jam’iyya yace ta haka ne za tabbatar cewar jam’iyyar APC ita ce jam’iyyar ‘yan Nijeriya da jihar katina kuma insha Allahu za a sami mambobin jam’iyyar fiye da tunanin jama a saboda a zaben da ya wuce an sami sama da mutum milyan daya da suka zabi jam’iyyar APC a jihar Katsina Kuma har yanzu jam’iyyar tana da dinbin magoya baya.