CRI Hausa" />

Akwai Fargabar ‘Yan Siyasar Amurka Za Su Lalata Kokarin Dakile COVID-19

A kwanakin baya ne babban daraktan hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya nuna damuwa kan matakan da wasu kasashe suke dauka, na adana allurar rigakafin cutar numfashi ta COVID-19 da ake fatan an samar, inda ya bayyana cewa, dole ne a kaucewa nuna fifiko kan al’ummun kasashe daban daban, yayin da ake raba allurar rigakafin annobar, kuma ya kamata a raba allurar ta hanyar da ta dace a fadin duniya, saboda hakan zai dace da babbar moriyar kasashe daban daban.

Hakika wasu ‘yan siyasar Amurka suna aiwatar da manufar nuna fifiko kan moriyar kansu, game da raba allurar rigakafin cutar, haka kuma suna gurgunta hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a bangaren yaki da annobar.
A halin yanzu, gaba daya adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a fadin duniya ya riga ya zarta miliyan 23. A cikin adadin kuma, akwai mutanen da suka rasa rayukan su sakamakon cutar da ya kai sama da dubu 800.
A karkashin irin wannan yanayi mai tsanani, ana kara mai da hankali kan tasirin allurar rigakafin cutar, kuma abun farin ciki shi ne, a kwanakin baya bayan nan, an samu babban sakamako wajen nazarin allurar a wasu kasashe, lamarin da ya samar da fata, da imani ga daukacin al’ummun kasashen duniya baki daya, amma abun bakin ciki shi ne, wasu ‘yan siyasar Amurka sun nuna burin kwace allurar. Har ma mujallar “Science” ta fayyace cewa, gwamnatin Amurka ta riga ta daddale yarjejeniyoyin sayen allurar rigakafin COVID-19 da darajarsu ta kai dala sama da biliyan 6, daga kamfanonin hada magunguna da dama.
Duk da cewa, an fahimci manufar gwamnatin Amurka, kasancewar Amurkar ce kan gaba wajen yaduwar cutar, amma sauran kasashe masu tasowa su ma suna bukatar allurar matuka, duba da cewa sun fi fama da karancin albarkatun kiwon lafiya.
Mujallar “The Ecologist” ita ma ta yi nuni da cewa, idan Amurka ta cimma burin kwashe allurar rigakafin da za a samar, to adadin allurar da za a samarwa kasashe masu tasowa zai ragu. Kaza lika babban daraktan cibiyar dakile cututtuka ta Afirka CDC Mr. John Nkengasong, shi ma ya nuna damuwa kan wannan batun.
Kamar yadda wasu masu yin sharhi kan al’amuran yau da kullum suka bayyana, ko da ma an yi nasarar samar da allurar rigakafin, ba zai yiwu a cimma burin ganin bayan cutar ba, sai an tsara yadda za a raba allurar, wanda hakan batu ne mai muhimmanci matuka ga kasa da kasa. Kuma ya dace kasashen duniya su kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu.
Babban daraktan hukumar WHO Tedros, shi ma ya nuna cewa, idan ana son ganin bayan cutar, dole ne a dakile ta daga dukkanin fannoni a fadin duniya, kana ba zai yiwu wasu sassa na duniya, ko wasu kasashe kalilan su cimma burin farfadowa daga tasirin annobar su kadai ba. (Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version