Daga Ibrahim Muhammad da Mustapha Ibrahim Tela, Kano
Kungiyar masu gidajen Biredi ta kasa reshen Jihar Kano, karkashin shugabancin sabon shugabanta, Alhaji Mu’azu, wanda aka fi sani da Alhaji Mu’azu Gidauniya Bread ta bayyana cewa taana da gidanjen biredi da ta yi wa rijista sun kai 7,400 a Kano kawai, wanda suke da matasa da suka dauka aiki sama da dubu 100, wanda suke aiki a sako da lungu na jihar Kano.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin mai ba kungiyar shawara ta fuskar shari’a, Alhaji Danladi Baba Kwanar Dawaki, wanda kuma shi ke da ‘Bilkisu Bread’ a lokacin da yake bayani a lokacin rantsar da shugaban kungiyar da sauran shugabanni a kungiyar a dakin taro na Central Hotel Kano, inda ya ce yanzu za su yi amfani da damar su wajen kawar da bata gari a wannan kungiya.
Kamal Muhammd Abubakar mai lakabin ‘Zamani Bread’ shi ne Babban Jami`i a kungiyar da ya Jagoranci gabatar da zaben, ya ce sun yi zabe cikin Nasara idan aka yi la`akari da wadanda aka zaba, kamar irin su Alhaji Alhasan Danhasan, shugaban Amintattu na kungiyar, wanda ya yi alwashin kawo sauyi mai ma`ana, musamman na su ga an rage tashin gwauron zabi na kayayyakin da ake hada biredi
A wata zantawa da ya yi da wakilanmu, Shugaban dattawan kungiyar ta masu gidajen Borodi, Alhaji Aminu Alhasan Danhasan ya bayyana cewa masu yin biredi a Kano, suna samar da aikin yi ga dimbin mutane, domin a cewarsa, in banda gwamnati ba wasu masu sana,a da suke bada aiki ga jama’a kamar kungiyar tasu.
Ya kara da cewa kungiyar tasu ta gudanar da zaben nana ne domin ci gaba da inganta harkokinta. Inda ya tabbatar da cewa Biredin da suke yi ya fi duk irin biredin da sabbin kamfanonin zamani ke yi a dadin dandano da inganci, sai dai kawai a nuna masu kyalkyali.