Mahdi M Muhammad">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Akwai Kyakkaywar Alaka Tsakaninmu Da ’Yan kabilar Ibo – Sarkin Bichi

by Mahdi M Muhammad
November 24, 2020
in LABARAI
2 min read
Akwai Kyakkaywar Alaka Tsakaninmu Da ’Yan kabilar Ibo – Sarkin Bichi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Mai Martaba Sarkin Bichi da ke Jihar Kano, Alhaji (Dr.) Nasiru Ado Bayero, ya nuna godiyarsa ga Gwamna, Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu kan zaman lafiya da al’ummar Arewa ke morewa a jihar a karkashin gwamnatinsa, ya na mai cewa, da ma can akwai kyakkyawar alaka tsakanin ’yan kabilar Igbo da Hausawa.

Sarkin na Bichi ya fada wa Gwamna Ugwuanyi cewa, jajircewar gwamnatinsa ce ta sanya hadewar kan ‘yan kasa da kuma zaman lafiya bakidaya a jihar Enugu ba tare da la’akari da kabila, addini da bambancin siyasa ba, “kuma ba za mu taba mantawa da wannan karamci ba, kuma za mu ci gaba da yi maka godiya har abada”.
Dakta Nasiru Bayero ya kuma yaba wa sarakunan gargajiyar a Jihar Enugu, inda ya jaddada cewa “bisa alakar ku da al’ummar Arewa a cikin kananan hukumominku, rahotanninmu da mu ke samu daga gare su na da matukar burgewa, don haka mu na matukar godiya sosai.”
Da ya ke magana lokacin da Gwamna Ugwuanyi ya yi masa maraba a gidan Gwamnatin Enugu, Sarkin wanda kani ne ga Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya yi amfani da wannan dama ya tabbatar wa gwamnan cewa “idan muka dawo Jihar Kano, za mu kare maslaha, kuma za mu tabbatar da cewa duk wani dan kabilar Ibo ko wani dan Nijeriya da ke zaune a Kano yana cikin kariya da kwanciyar kankali.
Ya ci gaba da cewa, “Dangantakarmu da tsakanin mu ta habaka fiye da da kuma ba za mu kyale wani abu mummunan yanayi ya bata wannan dangantaka ba”.
Saboda haka sarkin ya yaba wa Gwamna Ugwuanyi saboda karimci da salon mulkin ya nuna wanda ba a saba ganin irin shi ba wajen samar da zaman lafiya, tsaro, hada kan kowa da kuma shugabanci na gari.
Da yake bayyana ziyarar da ya kawo jihar ta Enugu a matsayin kamar ya dawo gida ne, ya ba da labarin dorewar dangantakar da mahaifinsa marigayi, Ado Bayeroya ke da ita tare da abokansa ‘yan kabilar Ibo, musamman lokacin da ya ke Shugaban jami’ar Nijeriya ta Nsukka (UNN) na tsawon sama da shekaru 20.
Ya kuma bayyana cewa, “ziyarar da ya kawo jihar zai gina kyakkyawar alaka a tsakanin Arewacin Nijeriya da wannan bangare na Nijeriya, Gabas”, yana mai jaddada cewa, “za mu ci gaba da gina wannan alaka, kuma za mu ci gaba da tabbatar da cewa Nijeriya ta kasance daya kuma duk da wadannan zai sa mu ci gaba da kasancewa ‘yan’uwan juna da yardar Allah.”

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Buhari Da APC Sun Yi Faduwar Bakar Tasa, Cewar PDP

Next Post

Tauye Dimukradiyya: Yadda Gwamnoni Suka Yi Wa Kananan Hukumomi Kamshin Mutuwa (4)

RelatedPosts

Gwamnan Bauchi Ya Amince Da Murabus Din Sakatarenshi

Gwamnan Bauchi Ya Amince Da Murabus Din Sakatarenshi

by Mahdi M Muhammad
2 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad...

Fitaccen Dan Jarida A Duniya, Larry King, Ya Rasu

Fitaccen Dan Jarida A Duniya, Larry King, Ya Rasu

by Mahdi M Muhammad
7 hours ago
0

Fitaccen mai watsa shirye-shiryen talabijin da rediyo, Larry King, wanda...

EFCC Ta Cafke ‘Yan Damfarar Intanet 11 A Osogbo

EFCC Ta Cafke ‘Yan Damfarar Intanet 11 A Osogbo

by Mahdi M Muhammad
9 hours ago
0

EFCC ta cafke wasu mutane 11 da ake zargi da...

Next Post
Rikice-rikice

Tauye Dimukradiyya: Yadda Gwamnoni Suka Yi Wa Kananan Hukumomi Kamshin Mutuwa (4)

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version