Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya bayyana cewa, akwai bangarori daban-daban wadanda suka kunshi kasashen Turai, Asiya da Afirika hadi da Kiristoci da Musulmi da ke daukar nauyin ayyukan ta’addancin Boko Haram.
Bugu da kari kuma, Gwamna Zulum ya ja kunnen ’yan Nijeriya su daina kallon halin da ake ciki na tabarbarewar tsaron a matsayin matsala ce wadda ta shafi yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya kawai.
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana hakan ne a taron shekara-shekara domin tunawa da babban dan fafitika, Cif Gani Fawehinmi karo na 17, wanda kungiyar lauyoyi ta Nijeriya (Nigerian Bar Association, NBA) ta shirya ranar Juma’a a Ikeja ta Jihar Legas.
Zulum ya sake nanata cewa masu daukar nauyin ayyukan Boko Haram daga waje, suna amfani da matasan yankin arewacin Nijeriya wajen aiwatar da wannan mummunar manufa ta kai hare-haren.
Bugu da kari kuma, Gwamnan ya yi kiran bai-daya ga yan Nijeriya da cewa su dena kallon rikicin Boko Haram a matsayin matsala wadda ta shafi yankin arewa maso gabas a jihohin Borno, Yobe da Adamawa ko yankin arewa kadai, su dauke shi a matsayin wanda ya shafi kowa.
“Dole mu dena kallon tabarbarewar tsaro a matsayin matsalar arewa kawai. Saboda idan mun yi la’akari da tazarar da take tsakanin jihar Borno zuwa Legas ya doshi kimanin kilomita 1,700, amma dole kaji cewa matukar babu kwanciyar hankali a jihar Borno to hakan zai shafi kowane sashen kasar nan.
“Kuma lokaci ya yi wanda ya kamata mu hada hannu wuri guda don mu yaki matsalar tsaro. Saboda kowanen mu ya ga abinda ke faruwa a kasashen Libya, Irak da sauran su. Bisa ga hakan, mu tashi tsaye wajen samar da dawamamen zaman lafiya da fahimtar juna a yankunan mu shi ne abu mafi muhimmanci,” in ji Zulum.