Connect with us

WASANNI

Akwai Matsala A Barcelona, Cewar Puyol

Published

on

Tsohon dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Carles Puyol, ya bayyana cewa kungiyar a halin yanzu tana cikin matsala bayan da suka kasa samun nasara akan kungiyar Celta Vigo a ranar Asabar din data gabata.

Barcelona dai ta raba maki da kungiyar ta Celta Vigo, bayan da ta tashi 2-2 a gidan Celta Vigo din a gasar La Liga da suka fafata ranar Asabar kuma dan wasa Luiz Suarez ne ya fara ci wa Barcelona kwallo bayan da Lionel Messi ya yi bugun tazara, amma sai Fedor Smolob ya farke bayan da Okay Yokuslu ya ba shi kwallo.

Suarez ne dai ya ciwa Barcelona kwallo ta biyu ta yi kyau sosai – kuma Messi ne ya ba shi kwallon sai dai kuma dan wasa Iago Aspas ya farke a bugun tazara ana saura minti hudu a tashi daga wasan.

Celta Vigo ta kusan kara kwallo ta uku daf da za a tashi wasa bayan da Nolito ya samu dama ya buga kwallo, amma sai ta je gurin Marc-Andre ter Stegen kai tsaye wanda shima ya dawo da kwallon cikin fili.

Messi, wanda har yanzu bai ci kwallo a wasanni uku na Barcelona ba yana da kwallaye 699 da ya zura a raga a wasan da ya yi wa Barcelona da tawagar Argentina  sai dai kwallo ta biyu da Suarez ya ci, Messi ya bayar da kwallo an zura a raga sau 250 a Barcelona kenan.

Messi, mai shekara 33 a duniya shi ne kan gaba a cin kwallaye da kwallo 21 a La Ligar bana, ya kuma bayar da 17 aka zura a raga nan ma shi ne na daya a bana sai dai Barcelona tana mataki na biyu da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid wacce  ta buga wasa ranar Lahadi da Espanyol kuma ta samu nasara.

Sai dai tsohon dan wasan baya na kungiyar ya bayyana cewa dole ne sai shugabannin kungiyar sun koma teburin shawara domin samu bakin zaren saboda abubuwa suna tafiya ba yadda aka tsara ba kuma akwai bukatar canja shawara.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: