Connect with us

WASANNI

Akwai Matsala A Brazil -Ribaldo

Published

on

Tsohon dan wasan kasar Brazil, Ribaldo ya bayyana cewa tabbas a kwai matsala a yanayin yadda kasar ta buga wasan farko na cin kofin duniya da kasar Switzerland wasan da aka tashi 1-1 a kasar Rasha a ranar Lahadi.
Brazil dai itace kasar datafi kowacce kasa yawan lashe gasar bayan ta lashe gasar sau biyar kuma rabon da kasar ta lashe gasar tun shekara ta 2002 wanda aka buga a kasashen Koriya da Japan lokacin da suka doke kasar Jamus.
Ribaldo ya ce babu wani matsayi da yawan wasan kasar zasuje indai ba matsayi na daya basu farantawa yan kasar rai saboda an san Brazil a kowacce gasar cin kofin duniya sune kasa ta farko da ake saran zasu lashe gasar.Mafi akasarin magoya bayan ‘yan wasan na Super Eagles sun nuna rashin gamsuwa da kamun ludayin Nijeriya a wasan da ta yi rashin nasarar da 0-2.
Tsohon gwarzon dan wasan Super Eagles Jay Jay Okocha, na daga cikin wadanda suka yi tsokaci kan wasan na ranar Asabar,inda ya dora alhakin kayen da Nijeriya ta sha akan rashin dabara a bangaren mai horarwa da kuma ‘yan wasan.
Okocha, wanda ya bayyana haka yayin zantawarsa da gidan talabijin na Super Sports, ya ce ‘yan wasan Nijeriya sun buga wasan ne a guraben da basu saba buga wasa ba, lamarin da ya sa suka gaza nuna bajintarsu.
Tsohon dan wasan na Super Eagles ya bayar da misalin cewa kama ta yayi, kaftin din tawagar Super Eagles Mikel Obi, ya buga bangaren dan tsakiya mai tsaron gida, kamar yadda ya ke yi a lokacin da yake kungiyar Chelsea, amma ba sashin dan tsakiya mai jefa kwallo ba.
Okocha ya kara da cewa Aled Iwobi, wanda a halin yanzu shi ne mafi kwarewar dan wasan tsakiya a tsakanin ‘yan wasan na Super Eagles, kamata ya yi a wasan na ranar Asabar, ya buga bangaren tsakiyar, amma ba gefe ba.
A ranar 22 ga watan Yuni da muke ciki Nijeriya za ta fafata da Iceland, yayinda kuma a ranar 26 ga watan za ta buga da Argentina.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: