Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KASUWANCI

Akwai Rufin Asiri A Sana’ar Surfe Da Niƙa –Kuta

by Tayo Adelaja
October 5, 2017
in KASUWANCI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Editan Kasuwanci Mohammed Shaba Usman  08030617599

Alhaji Muhammdu Jibo Kuta, shi ne shugaban ƙungiyar masu surfe da niƙa ta jihar Neja, a tattaunawarsa da wakilinmu Muhammad Awwal Umar ya yi tsokaci akan yadda ƙungiyar ta tsere sauran ƙungiyoyi. Ga dai tattaunawar.

samndaads

Da farko za mu so jin taƙaitaccen tarihin rayuwar ka?

Sunana Muhammad Jibo Kuta, an haife ni a shekarar 1963, na yi karatun Firamarena da sakandare, daga bisa ni na tafi kwalejin horar da Malamai. Sannan kuma na yi Difloma akan aikin jarida. Na yi karantarwa tsawon shekaru goma sha takwas, daga bisani na canja sheƙa zuwa aikin jarida, wanda yanzu ina da shekara goma da ɗoriya a aikin jarida har na kai muƙamin mataimakin Edita.

Lallai hakka ne! Na taso ina ƙaramin na iske mahaifina na sana’ar gini, noma kuma da niƙa, duk da cewar ina noman, amma ban mayar da shi sana’a ba kuma shi aikin gwamnatin ba na dogara akan shi ba ne, duba da yadda na ga ma’aikatan gwamnati na ƙarewa a rayuwarsu bayan barin aikin. Yau ina da shekara 35 ina sana’ar niƙa, domin na fara tun 1976 da injin mahaifina, ga shi yanzu ina da injinan surfe har guda uku.

Wani abu da ya daɗe yana ci min tuwo a ƙwarya shi ne idan na yi ritaya a lokacin da ƙarfina ya ƙare, noma zai iya riƙe ni kuwa, sai na ga dacewar in samu wani abu da zai zama tallafi ga rayuwata, ita sana’ar nan ta niƙa tana da albarka kuma ana samun alheri a ciki, sai na fara tunanin yadda za mu bunƙasata ta yadda za ta zama mai anfani gare da sauran jama’a.

Kamar ya ke nan?

Yau, na duba kusan matasan mu kashi tamanin da biyar, ko dai sun yi boko babu aiki, ko kuma ma ba su samu daman yin karatun ba, kuma suna buƙatar kulawa dan dogaro da kansu. In ko haka ne, akwai buƙatar ƙirƙiro wata hanya da za ta zama mai amfani. Kasancewar na riƙe muƙamin shugaban ƙungiyar a Ƙaramar Hukumar Bosso na tsawon shekaru takwas, sai ya ba ni damar faɗaɗa tunina, wanda hakan ya sa bayan kafa ƙungiyar a matakin jiha na samu nasarar zama babban sakataren ƙungiyar, bayan wani ɗan lokaci kuma sai aka yi zaɓe na zama shugaban ƙungiyar a matakin jiha.

A farkon shekarar aka yi zaɓe aka kuma rantsar da ku, zuwa yanzu kuna da wani abin nunawa?

Ƙwarai kuwa, mu ke da abin nunawa, domin daga kafa wannan ƙungiyar zuwa yanzu, waɗanda muka yi wa rajista a ƙarƙashin ƙungiyar mutum tamanin ne a halin yanzu suka ci amfanin ƙungiyar, burinmu kafin shekarar ta ƙare, mun yaye matasa ɗari da ashirin da biyar zuwa da hamsin a ɓangarori daban-daban na sana’ar niƙa da surfe.

Amma kafin mu yi nisa, ita ƙungiyar lokacin da kuka kafa, akwai wani da ke ɗaukar nauyinta ne?

Sai muka yi nazarin fara sayen masara muna bayarwa ga ‘yan kasuwa, hakan ya ba mu damar kafa ƙungiyar mata masu sayar da garin masara da dawa na mutane 42, a lokacin ana sayar da masara akan naira dubu goma sha takwas mu kuma idan mun ba su a ƙarshen sati idan sun sayar za su ba mu naira dubu ashirin ne akan kowane buhun masara. Tsarin shi ne a ƙarshen shekara za mu yi lissafin ribar da aka samu sai a baiwa kowa rabon shi, uwar kuɗin nan za mu ci gaba da juyawa a matsayin jarin mu.

Ganin ba kowane mamban ku ne yake cin wannan ribar ba, ko su sauran wani tanadi kuka yi masu?

Abin da muka yi, lokacin da muka zo mun iske ana sayar da buhun dussa dubu ɗaya da ɗari biyar zuwa da ɗari shida, matuƙar tsadar dai dubu biyu ne, sai muka shiga muka fita muka yi yarjejeniya da wasu kamfanoni masu sayen dussa daga jihar Sokoto, Kwara da Legas ta yadda za su riƙa samun dussa mai tsafta, muka ɗaga darajar dussan har ya kai dubu takwas a lokacin baya, ko yanzu da masara ta yi sauƙi ba, mu yarda darajar dussa ta kasa kai dubu huɗu ba. Ka ga su ma sauran an tallafa masu ta nan.

Ganin kamar hanyar samun kuɗin shigar ba zai iya wadatar da ku ƙudurce-ƙudurcen ku ba, ko akwai wata dubara nan gaba?

Ai ba gaba ma, yanzu haka mun ƙirƙiro wasu hanyoyin guda uku da zai ƙara ɗaga darajar ƙungiyar da hanyar samun kuɗin shiga ma. Na farko kana iya shigowa a matsayin mai sana’a ka zuba dukiyar ka tana kawo ma kuɗi a kullun kuma mu ma a ƙungiyance muna ƙaruwa da kai, hanyar kuwa ita ce ka ba da kuɗi a kafa injin, mu zamu riƙa sanya ido wajen shigar kuɗin kai na ka shi ne ka ba mu asusun ajiya, ya danganta sati ne ko wata, za a riƙa zuba mana ka kason a cikin asusun ajiyar. Muna da Lauya da zai zaunar da kai a yi tsarin, sannan idan kana da kuɗi ba su isa kafa injin ba, muna buƙatar dubu ɗari shida a hannun ka, idan mun kafa injin ga kasonka a kullum, ko wata ne, ko sati, ya danganci yadda aka yi tsarin. Ka ga nan ma kuɗin shiga na isowa a cikin aljihun ƙungiya. Sannan wanda yake son koyon sana’ar ma yana da daman kafa injin mu kula mai da shi, amma akwai abin da za a riƙa ware wa ƙungiya, ka ga hanyoyin samun kuɗin shiga sun ƙaru ke nan ko.

Sai na ga kamar mambobin ku kashi biyu ne, misali waɗanda ke cikin gari suna amfana da wutar lantarki yayin da waɗanda ke karkara sun fi mai da hankali akan aiki da injin mai amfani da mai?

Ai yanzu kusan da na cikin garin da na karkara kowa na amfana da wutar da kuma injin mai. Abin da muka yi shi ne, idan ba wuta za a yi amfani da injin mai mukan ɗan ƙara farashin aikin saboda tsadar mai, su kuma mutanen da ke cikin karkaru dama biyu suka samu, domin yanzu idan muka fahimci wayar wuya ya ratsa a karkara mukan shirya da ma’aikatan wuta sai a sauke wuta a gari mu, kuma mu baiwa masu injin niƙa bashin tiransfoma. Mun shirya wannan da kamfanonin da muke ciniki da su ne. Ko a makon nan mun karɓi transifoma mai girman 500kb, inda muka yi yarjejeniya da masu surfen, kowane mako da adadin buhun dussar da za su bayar har a kammala biyan kuɗin tiransifoma ɗin. Ka ga sun samu wuta a sauƙaƙe suna sana’a, kuma karkarunsu al’umma za su amfana da su saboda sauke tiransifoma da aka yi.

Ganin kamar duk wannan bayanin da ka yi akan shugabancin jiha ne, ko ya abin yake ne?

Ai ba ka sani ba, yanzu haka muna da shugabancin shiyya da ya ƙunshi Neja ta Kudu maso Gabas, da Neja ta Tsakiya da Neja ta Arewa. Sannan kwanakin nan muka rantsar da shugabannin Ƙananan Hukumomi takwas cikin ashirin da biyar da muke da su. Sauran kuma muna bin su a hankali, kuma su ma za mu rantsar da sauran shugabannin sauran Ƙananan Hukumomi nan ba da jimawa ba.

Idan na fahimce ka, kamar akwai gurabu da dama da za a iya amfana da su ta hanyar surfe da niƙa?

Wannan maganar haka take, ka gane sirrin da ke cikin wannan sana’ar yana da yawa, domin yau mun wayi gari bankuna ne ke bin mu da nufin mu karɓi bashi saboda alheran da ke cikin sana’ar surfe da niƙa. Yau idan matashi ya zama mai haƙuri, in dai ba zai sa haɗama ba, in har zai rungumi wannan sana’ar, to lallai zai samu rufin asiri ba tare da ya sha wahala ba. Na farko dai ba a yin ritaya balle a ce an kai shekarun barin sana’a, kuma wata dama ce da za ta iya taimaka wa magidanci na sauƙin rayuwa tare da iyalansa, sannan sana’a ce da za ka riƙa biyan buƙatun na yau da kullun ba tare da tunanin faɗuwa ba in dai ba a matsantawa kai ba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Amfanin Namijin Goro A Jikin Mutum

Next Post

SHAFIN FARKO

RelatedPosts

Sugar

Alakar Dake Tsakanin Sukari Ca Ciwon Suga

by Muhammad
2 months ago
0

Da yawa a yankin kasashen nahiyar Afirka ana ganin sukari...

A Na Cigaba Da Zaman Doya Da Man Ja Tsakanin Majalisa Da Shugaba Trump

Ba Da Mugun Nufi Shugaba Buhari Ya Garkame Iyakoki Ba – Ministar Kudi

by Abdulaziz Kabir Muhammad
1 year ago
0

Ministar kudi da tsaretsare, Uwargida Zainab Ahmed Shamsuna, ta sanar...

Gwamnatin Tarraya Ta Kebe Biliyan N2.6 Don Aikin Tashar Mambilla A 2020

by Abdulaziz Kabir Muhammad
1 year ago
0

Sama da shekaru arba’in da suka shude kenan da bada...

Next Post

SHAFIN FARKO

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version