Rabiu Ali Indabawa" />

Akwai Sauran Rina A Kaba: Rikicin Iran Da Amurka

Jiya Litinin Shugaban Amurka Donald Trump ya kakaba ma Kasar Iran abin da ya kira takunkumi mai zafin gaske na tattalin arziki, wanda takamaimai ya fi shafar Shugaban addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Trump ya rattaba hannu kan umurninsa na Shugaban Kasa wanda ya ce zai hana Khamenei da Iran harkar cinikayya da duniya. Sakataren baitilmalin Amurka Stebe Mnuchin ya ce, wannan mataki ne da zai tsaida kadarorin biliyoyin daloli na Iran.

Trump, ya kira wannan umurnin na shi “Mai karfi kuma wanda ya dace” a matsayin martanin Amurka ga kakkabo jirgi marar matuki na Amurka da Iran ta yi a makon jiya. Amurka ta ce jirgin na tafiya ne a yankin sararin sama na Kasa da Kasa, daura da Hormuz, amma ita Iran ta ce jirgin ya shiga yankin sararin samanta.

Saura ‘yan mintoci kawai jiragen Amurka su yi barin wuta kan Iran ranar Alhamis, sai Shugaba Trump ya yanke shawarar cewa ba zai dau irin wannan matakin sojin ba saboda harbo jirgin Amurka mara matuki da Iran ta yi, bayan da aka gaya masa cewa harin na iya sanadin mutuwar Iraniyawa kimanin 150.

Yayin da yake jawabin sanarda wannan takunkumin, Trump ya ce, “Ina ganin mun nuna matukar hakuri, amma ba lallai bane mu kara daurewa irin haka a gaba. Amma za mu gwada yanzu.” Wani labari mai kama da haka kuma, Shugaban Kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewar Kasarsa ba ta bukatar gwabza yaki da Amurka, amma kuma za ta kare kanta duk wani lokacin da aka nemi afka mata.

Rouhani ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da shugaban Faransa Emmanuel Macron ta waya, inda ya jaddada matsayin kasar na cewar bata bukatar yaki da duk wata kasa.

Shugaban na Iran ya bayyana cewar Kasar sa na cigaba da goyan bayan zaman lafiya a yankin tekun Fasha da ma duniya baki daya. Sakamakon takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran, Kasar ta yi barazanar ficewa kacaukan daga yarjejeniyar nukiliya daga ranar 7 ga watan gobe. yayin da Faransa ke gargadin ta kan daukar matakin.

Shugaba Macron wanda ya sauka a Osaka dake Kasar Japan domin halartar taron Kasashen G20 ya bayyana cewar zai tattauna da shugaba Donald Trump na Amurka kan batun Iran.

A bangare guda kuma, Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi Iran da cewa za ta dandana kudarta muddin ta kuskura ta kai wa Amurka ko kuma muradunta hari, domin za ta maida raddin da ka iya ruguza Kasar ta Iran.

A Gargadin na Trump da ya wallafa a Shafinsa na Twitter ya ce shugabannin Iran ba sa fahimtar komai idan ba an nuna musu karfi da iko ba. Wannan na zuwa bayan da Sakataren Tsaro na Amurka John Bolton ya gargadi Iran da kada ta sukurkuta taron sulhu game da Gabas ta Tsakiya da aka fara yau a Bahrain.

Yayin wata ziyara John Bolton ya bayyana cewa, Iran na ta wasu take-takenta, tare da yi wa Amurka tsiwa, domin hatta taron da ake yi a Bahrein karkashin jagorancin Amurka, Iran na iya yin katsalandan a ciki. A makon jiya ne dai Iran ta kakkabo wani jirgin sama na Amurka maras matuki a ciki, da ya ratsa sararin samaniyarta, zargin da Amurka ta musanta.

Amurka a nata bangaren ta zargi Iran da laifin kai hare-haren ta’addanci kan jiragen ruwa dake dakon albarkatun mai a yankin Gulf, zargin da Iran itama ta musanta. A yau ne dai ake fara wannan taro a Manama dake Bahrein wanda Amurka ta shirya da niyyar gabatar da wasu tsare-tsaren bunkasa tattalin arzikin yankin duk dai don ganin an samu zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falesdinawa.

Karkashin tsarin za’a zuba kudaden da suka kai bilyan 50 na dalla cikin shekaru 10 a yankin Falesdinawa da kasashen Larabawa dake kusa.

Exit mobile version