CRI Hausa" />

Akwai Tabbaci Ga ‘Yancin Bin Addini Na Al’ummar Kabilu Daban Daban Na Jihar Xinjiang

Kakakin ofishin watsa labaru na gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai ta kasar Sin, Elijan Anayit, ya bayyana cewa, tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya yi wasu kalamai na karya, game da hakkin bin addini a jihar Xinjiang, da nufin tayar da fitinar kabilanci a jihar, tare da kulla mummunar aniya.
Elijan ya ce, alal hakika, ana matukar girmama ‘yancin bin addini na dukkan kabilun da ke jihar Xinjiang.
Kakakin ya bayyana haka ne a a gun taron manema labaru da jihar ta shirya a yau Alhamis, kan maganganu marasa ma’ana da Pompeo ya yi a kwanan baya. Kakakin ya kara da cewa, ayyukan addini da dukkan musulmai na kabilu daban daban a jihar suke yi yadda ya kamata a masallatai da gidajensu, kamar karanta Alkur’ani, da yin salloli, da wa’azi, da azumi, da yin bukukuwan musulunci, ana aiwatar da su baki daya gwargwadon yadda suke, kuma doka ta ba su kariya ba tare da tsangwama ba.
Ban da wannan kuma, a watan Maris na shekarar 2019, majalisar ministocin harkokin waje, ta kungiyar hadin kan Musulunci, ta zartar da wani kuduri, wanda ke jinjinawa kokarin da kasar Sin ke yi, a fannin kula da musulmai. (Mai fassara: Bilkisu)

Exit mobile version