Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Asabar. Hakika na yi farin ciki da kirkiran wannan shafi na musamman domin masoya tare da isar da sakon da muke son isarwa ga ‘yan’uwa masu gudanar da soyayya. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jini baki daya.
Lalle ne a cikin zamantakewar soyayya akwai wasu abubuwa da masoya ba su so sa’ilin hira a tsakanin su. Da yawan masoya na korafi kan masoyansu duk da cewa matsalolin na da yawa amma zan dan yi duba a kan wasu daga ciki.
Matsalar ta farko ita ce, wani namijin ya tsani jira yayin da ya je zance wajen budurwarsa, wannan dadewar tana saka masa kuna a cikin zuciya koda kuwa ya zo tare da farin ciki. Wasa mazan suna kasa jurewa sai su kira hakan da wulakanci.
Yana da kyau ‘yan uwana mata da su yi hakuri, su rage yawan jinkiri a lokacin da masoyansu suka zo domin faranta musu zuciyarsu, don wata ta san zai zo, maimakon ta shirya tun kafin ya zo sai ta ki. Sai bayan ya zo za ta fara shiryawa. Wata ma a lokacin za ta shiga wanka, sai ya gama bata lokacinsa idan yana da wani uzirin nasa ma sai ya hakura ala dole tun da kin bata masa lokacin da ya gama lissafa a kan abubuwan da zai yi a wannan ranar. Sai dai kawai ya danne zuciyarsa ya nuna miki hakan babu damuwa saboda yana son ki, amma yana cikin damuwa.
Ita kuwa ta yi ta washe baki babu wadda yake so sama da ke kuma ba za ki canja ba. Ki sani a duk lokacin da ya samu wadda ta fi ki iya soyayya da nuna kulawa barin ki zai ya koma wurin ta. Ko kuma ku yi ta samun matsala da shi saboda kina kona masa zuciya, koda a ce ba kya son sa akwai hanyoyin da za ki bi domin ku rabu lafiya ba tare da wani cutarwa ba.
A wani bangaren kuma wata macen takan fito zance tana taunar cingam, wanda maza da yawa sun tsani hakan, idan wani na son hakan to wani ba ya so, a nawa tunanin ma babu wanda zai so hakan, a kan kanki ma idan kika yi tunani sosai za ki iya gane cewa matsayinki na ‘ya mace mai tarbiyya wadda ta taso cikin al’adar malam bahaushe yin hakan ba dai-dai ba ne.
Wani namijin daga wannan halin da ta nuna masa zai ji soyayyarta ta fita a ransa koda kuwa akwai sauran son da yake mata, ya kan kasa sanin yadda zai fito ya fada mata matsalar ta wanda ita a nata tunanin dai-dai ne kuma ba dai-dai ba ne.
Bari na dada kara hangawa a wani bangaren da yawan maza ba sa son su je zanje kuna hira ki ta ce masa (uhmm…), ko kuma (ina ji), shi ma hakan maza da yawa ba sa bukatar sa. Shi namiji yana so ki bude baki ki yi masa magana kar ki ce ‘yin hakan ai zubar da aji ne’ ko kadan da yawan matsaloli na soyayya akwai abun da in har kin yi su ba zub da aji ba ne.
Har ila yau, su ma mazan ya kama su fahimta cewar a cikin mata akwai wadanda ba su da yawa daga halayen ku. Wata macen ba ta son maimaita zance kullum, ka zo zance hirar da za ka yi mata ta wancen zuwan da ka yi ne, yana da kyau kafin ka je zance ka tsara abin da za ka fada mata wanda za su sanyaya mata zuciya, ya sa ta farin ciki ta tuna da kai yayin da ka koma gida har ma a wani lokaci ya sakata yin mafarkin ka.
Kar ka zo kai mata hiran kwallo ko kuma duk ma abin da ya shafi kwallo, idan namiji na yi wa mace hirar kwallo, to mace za ta tsane shi a wajen zance wani lokaci har ma a cikin zuciyarta, duk da dai wasu matan su ma ‘yan kwallon ne, to amma dai da yawan mata ba sa bukatar irin wa ‘yan nan hirar yayin da suke tare da masoyansu, ko hirar biki ko ta fim da dai sauran su, sai a tsaya a yi tunanin hirar da ta shafi masoyiyar ko masoyin wajen yaba halaye da kyawu da kuma yadda za a tsara rayuwa da sauransu, hakan shi yake kara kaunar juna tare da tuna juna a koda yaushe.
Lalle akwai masoya da dama da suke tafka kuskure wajen yin zance. Ya kamata mu dauki darasi a kan wannan dan tsokaci da na yi mata a cikin matsalolin a wajen zance. Na san cewa, akwai abubuwa da dama wadanda masoya ba su so lokacin hira, amma na kawo kadan daga cikin su. Sai mu yi kokarin kiyaye wa domin mu samu kyakkyawan fahimta ga masoyanmu ba tare da samun wani matsala ba.
Sakon soyayya daga masoyinku Mahmud Sani, KD
08151693170