Dan wasan gaba na Manchester United, Edinson Cavani, zai fuskanci hukuncin dakatarwar wasanni uku daga Hukumar Kwallon Kafa (FA), idan aka same shi da laifin amfani da kalaman wariyar launin fata ko nuna wariya a shafukan sada zumuntarsa.
FA na bincikar asusun sakon sada zumunta na cavani dan asalin kasar Uruguay, wanda ya aika sakon bayan nasarar da suka samu a ranar Lahadi akan Southampton.
Cavani ya yi amfani da kalmar “gracias n ******” don godewa wasu masoyanshi da suka yaba kwallayensa biyu da ya zura a raga.
Matashin mai shekaru 33 daga baya ya goge rubutun, amma har yanzu yana iya fuskantar tuhuma.
An ba Bernardo Silva, hukuncin dakatarwa da buga wasa daya duk da cewa daga baya ya goge rubutun da yayi wanda ya kwatanta dan wasan kungiyar Manchester City, Benjamin Mendy, da wata alawa ta Spain.
Binciken na FA zai duba Dokar E3, wanda ke kunshe da rubuce-rubuce game da asalin mutum, launin fata ko kuma asalin kasa.
Bai Kamata Mu Yi Rashin Nasara A Hannun Manchester Ba, Cewar Klopp
Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool,...