Connect with us

LABARAI

Akwai Yiwuwar Dakatar Da Aikin Hajjin Bana, Inji Minista

Published

on

Kasar Saudiyya na Neman shawarar Malamai kan yiwuwar dakatar da gudanarwar aikin Hajjin Bana Saboda Cutar Korona ta kasashen Duniya
A karon farko ke nan za a yi fashin aikin Hajji a sama da shekaru 100 saboda annaobar, muddin ba ayiba a bana.
Allah Ya sa kada cutar Korona tahana aikin Hajji!
Ministan Ayyukan Hajji da Umara Saleh bin Taher Banten ya shaida wa gidan talbijin na kasar cewa mahukuntan kasar na ba da muhimmanci matuka ga rayuka da lafiyar mahajjata.
“Mahukuntan Saudiyya a shirye suke su kare lafiyar Musulmi a fadin duniya, don haka muke kira ga maniyyata su dakata har sai an fitar da matsaya”, inji ministan.
Saleh bin Taher Banten yana daga cikin manyan masu ba da shawara kan al’amuran aikin Hajji da Umara na duniya wanda yake da ra’ayin jinkirta har sai an kai lokacin da za a iya fahimtar tasirin annobar ta Korona

Advertisement

labarai