Connect with us

LABARAI

Akwai Yiwuwar Samun Sabuwar Annoba A Nijeriya – Minista

Published

on

lafiya

Akwai yiwuwar samun sabuwar buraguzan annobar Korona a kasar nan, Ministan Lafiya Dakta Osagie Ehanire, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis.

Ministan ya ce: “Dangane da buraguzan annobar Korona, tabbas a lokacin da ‘yan Nijeriya suka fara komowa tawaga-tawaga daga kasashen Duniya daban-daban misali daga kasashen Amurka, Saudiyya, Turai, China da sauran su, inda wasunsu duk an samu annobar ta korona a tare da a gwajin da aka yi masu a can kasashen.

“Tambayar a nan ita ce, ko buraguzan cutar ta korona da su ke dauke da ita daya ce da wacce muka sani a baya?

“Masu bincike sun tabbatar da cewa duk daya ce da irin kacce take yawo a kasashen Italiya da China. A nan muke tambayar ko akwai matsala dangane da mutanan da za su zo daga wasu sassan.

“Ba ni da wani bayani a kan hakan ya zuwa yanzun, amma ana tsammanin lallai ita ce.

“Dangane kuma da maganin gargajiyar kasar Madagasca, har yanzun ba mu da wani bayani a kansa tukunna. Mun mika maganin a hannun cibiyoyin bincikenmu suna nan kuma suna yin aiki a kansu. Ba wanda ya kawo mana wani sakamako tukunna. Amma ina ganin bayan dan wani lokaci zan sake tuntubarsu domin na ji ko akwai wani bayani a kansu.

Babban daraktan cibiyar kula da cutuka masu yaduwa, (NCDC), Dakta Chikwe Ihekweazu, ya kara da cewa: “A tsakanin karshen makon nan zuwa yau (jiya) mun rarraba kayayyakin kariya mafiya yawa tun daga lokacin barkewar wannan annobar.

“Kaso na karshe na kayayyakin kariyar ne za mu fitar da su a yau din nan, saboda ina son fitar da su kafin ranar hutu a gobe, duk kuma wani abu da muke yi muna yinsa ne domin mu taimaka wa Jihohi.

“Jihohi masu yawa suna gudanar da na su da kansu. Da yawan wuraren gwaji kamar a Jihohin Ekiti da Jigawa duk gwamnatocin Jihohin ne suka gina su domin su taimaka wa kansu.

Za kuma mu cigaba da yin aiki hannu da hannu da gwamnonin Jihohin domin inganta yaki da wannan annobar a kasar.

Advertisement

labarai