Akwai Yiwuwar Saudiyya Ta Dage Haramcin Kiran Waya

Saudiyya za ta dage haramcin kiran waya ta Intanet ciki har da kiran waya ta bidiyo da Skype da kuma WhatsApp, a wani mataki na bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ma’aikatar yada labaran kasar ta ce daga ranar Laraba, kowane dan kasar yana da damar yin kira ta amfani da manhajar Protocol (BoIP).

A baya dai ma’aikatar ta toshe manhajar ta BoIP, a cewar su, saboda ba a bin tsari da dokokin kasar.

Sanarwar na zuwa ne kwana biyu kacal bayan shafin sada zumunta na Snapchat ya toshe kafar yada larabari ta Al Jazeera a Saudiyya.

Hukumomin Saudiyyar sun zargi Al Jazeera da yada farfaganda da yada labaran da suke darsa tsattsauran ra’ayi a zukatan al’umma.

Tuni  Al Jazeera ta musanta dukkan zarge-zargen da aka yi mata, tare da cewa matakin da Snapchat ya dauka ya bayyana karara ana kokarin hana ‘yancin fadar albarkacin baki, da hana ‘yan jarida gudanar da ayyukansu yadda kamata musamman kan labaran da suka shafi yankin Gabas Ta Tsakiya.

Tun a karshen watan Mayu ne Saudiyya ta toshe shafin internet na Al Jazeera, kwanaki kadan gabannin kasashen yankin Gabas Ta Tsakiya su yanke alaka da kasar Katar bisa zargin taimakawa kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Fiye da manyan malamai 20, da marubuta, da ‘yan jarida, da malaman jami’o’i, da masu fafutukar kare hakkin ‘yan Adam ake tsare da su a Saudiyya tun daga farkon watan nan.

Kuma dukkansu suna da alaka da kokarin daidaita rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin kasashen Saudiyya, da Masar, da Bahrain da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa da Katar.

Tun bayan kadawar guguwar sauyi a yankin Gabas Ta Tsakiya, Saudiyya ta kara tsaurara matakan tsaro da sanya ido kan kafafen sadarwa na zamani.

Hukumomin sun yi ikirarin suna amfani da wata manhaja da ke ba su damar shiga shafukan ‘yan kasar kuma sun yi nasarar shiga shafuka 400,000.

Kamfanonin sadarwa sun ce tun a shekarar 2013 ma’aikatar sadarwa da nadar bayanai ta Saudiyya ta ce dole su bayar da hadin kai da bin dokokin kasar da kuma bibiyar shafukan sada zumunta na ‘yan kasar don sanin abin da suke ciki.

Kamfanonin dai ba su kara dogon bayani ba, amma dai abin da suka dage akai shi ne gwamnati na kokarin kare ‘yan kasar ne daga ayyukan ‘yan ta’adda da sauransu.

Sai dai a yanzu ma’aikatar sadarwar kasar ta ce, matakin bai wa ‘yan kasar wannan dama na zuwa ne bayan dogon nazari da bincike don ganin matakin bai cutar da ‘yan kasar ba musamman ma dai matasa.

Kuma mataki ne da zai kara bunkasa tattalin arzikin kasar, yawancin bakin da suke shiga Saudiyya sun fi amfani da kafafen sadarwa na zamani da kiran waya ta internet da sauransu, da hakan wani tagomashi ne da zai karawa tattalin arzikin kasar.

 

Exit mobile version