Daga Abba Ibrahim Wada
Kungiyar kwallon kafa ta Al Ahly ta kasar Masar ta lashe kofin zakarun kungiyoyi na Afrika bayan da a ranar Juma’a ta doke kungiyar kwallon kafa ta Zamalek da ci 2 da 1 kuma wasan ya hada kungiyoyin Masar biyu a filin wasa na Cairo ba tare da an baiwa yan kalo damar shiga ba saboda da cutar Korona dake ci gaba da halaka rayukan jama’a.
Wannan ne dai karo na 9 da kungiyar ta Al Ahly ke lashe kofin zakarun Afrika,wanda zai kuma baiwa kungiyar damar wakiltar Afrika a gasar cin kofin Duniya na kungiyoyi da hukumar kwallon kafar Duniya Fifa ta shirya a watan Fabrairun shekarar 2021 a Doha na kasar Katar.
Dan wasa Amr El-Soleya ne ya fara zurawa kungiyar Al-Ahly kwallonta ta farko a raga kafin daga bisani dan wasan gaba na Zamalek Shikabala ya farke kwallon kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Nasarar da Al-Ahly ta samu a wasan yasa yanzu tana da gasar sau tara kuma mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Pitso Mosimane ya zama mai koyarwa na uku kenan daya lashe gasar sau biyu da kungiyoyi daban-daban.
Wasan karshen dai an fafata ne a babban filin wasa na kasar Masar wato Cairo International Stadium dake babban birnin kasar kuma duka kungiyoyin biyu ‘yan kasar Masar din ne said a an buga wasan babu magoya baya kamar yadda hukumar kula da gasar ta tsara.