Zubairu T M Lawal" />

Al-Makura Na Yaudarar Kanshi Ne A Neman Sanata, Inji Shugaban PDP

Shugaban Jam’iyyar adawa ta PDP dake Jihar Nasarawa Hon.Francis Orugu ya bayyana haka yayin hira da manema labarai a ofishinsa da yake maidamartani ga Gwamna Umar Tanko Al-makura.

Ya ce; koda Al-makura yake cewa Jam’iyyar PDP ta mutu a Jihar Nasarawa da yaso da ya karbi ofishin PDP ya maidata ofishin APC. Orogu ya ce; Al-makura ya sani PDP Jam’iyya ce ba kungiya bace da tayi hadehade kamar APC. Ya ce; APC kungiya ce da kowa ya zo da manufarsa saboda a ture PDP a kafa Gwamnati ya ce;Allah yabasu sa’a sun ture PDP sun kafa Gwamnati amma Gwamnatin ta kasa tsinanawa alumman kasa komai banda bala’i da tsadar rayuwa.

Orogu ya ce; ya kamata Al-makura yasani alumman Jihar Nasarawa basu bukatar Jam’iyyar APC saboda bata da alheri.

Ya ce; Jihar Nasarawa ita ce kadai Jihar da Shugaban kasa Muhammad Buhari yake alfahari da ita tun ana CPC nan ne yake da Gwamna amma a tarihinsa bai tabayin nasara ya lashe zabe a Nasarawa ba. Ya kara da cewa Al-makura ba dan siyasa bane kuma ya daina cewa shine na dan Muhammad Buhari na gaskiya saboda ko da yaushe a ka yi zabe bai taba kare Martaban Buhari a Nasarawa ba kansa kawai ya sani.

Hon. Orogu ya ce giyan mulki yana bugarda Al-makura idan ya kwanta a gidan Gwamnati baya tunanin wani hali alumman Jihar Nasarawa suke ciki shiyasa yake maganganun rashin kwakwalwa.

Ya manta cewa yan Majalisar Tarayya da muke dasu guda Takwas daga Jihar Nasarawa biyar PDP ne uku ne APC shima Abdullahi Adamu daga PDP ne bayan ya ci zabe ya gudu ya koma APC.

Ya kara da cewa; Al-makura yana yaudarar kansa ne da yake neman Sanata ya sani wadanda suka fishi farin jini su ka yi aiki na gari sun tsaya neman Gwamna sun fadi bare shi da babu abin alheri da yayiwa jama’a kumama bashi da ruwan wanda ya dace ya zama Sanata.

Shugaban Jam’iyyar PDP ya kara da cewa batun samar da Labin shanu da Gwamna Umar Tanko Al-makura ke kokarin yayi a yankunan Doma Keana  da Asakio.

Ya yi tunani idan abin alheri ne me ya sa bai yi a garinsu ba.

Ya ce; ai ya kawo ci gaba a kauyensu duk da cewa kauyensu duk jama’an dake ciki basuwuce mutum dubu uku ba. Amma yana gina filin jirgin sama a garin ga Ofishin EFCC ga Makaranta Mata ga Asibiti ga kasuwa da sauransu me ya sa bai gina wadanan a wasu guraren ba ya gina a dan karamin kauyensu da babu mutane.

Amma yanzu yaje wasu guraren zai karba masu gonaki wai zai samar da Labin Shanu?

Ya samar da Labin Shanu a garinsu mana idan ci gabane ya kawo?ko garin nasu ya cikane. Ina ce bada dadewa bane alumman kauyensu su ka yi bore saboda an zo za a kwace masu fili a gina gadajen Gwamnati suka ce ba su yarda ba.

Exit mobile version