Daga Abubakar Abdullahi, lafia
Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawa ya shawarci mazauna jihar da ‘yan kasa baki daya da su guji furta kalamun kiyayya da kuma tada hankalin al’umma domin kawo cigaba.
Gwamna Al-Makura ya bada wannan shawarar ce a yayin taron jana’izar marigayi Abaga Toni na masarautar Toni, Dakta Sylbester Ayih, a gari Garaku da ke karamar hukumar Kokona a jihar.
Ya ce kowane dan Nijeriya na da ‘yancin zama a ko’ina a fadin kasar nan, kuma zaman lafiyar Nijeriya na da muhimmanci ga kowa domin haka ya wajaba ga kowane dan kasa ya karfafa zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya a kodayaushe.
Yayin taron, gwamnan ya bayyana ta’aziyyarsa da cewa, “Muna bayyana ta’aziyyarmu ga iyalan Abaga Toni da masarautar Toni da mabiya darikar Katolika da kuma jama’ar jihar baki daya dangane da wannan babban rashin da aka yi na Abaga Toni Dakta Sylbester Ayih wanda a halin rayuwarsa ya kasance mai karfafa zaman lafiya”.
Tare da cewa, “Babu sashi na al’umma da ba ya jimamin wannan rashi na basaraken gargajiya mai daraja saboda ya amfani rayuwar jama’a da dama domin marigayin mutum ne mai daukar kowa a matsayin abokinsa, ga karfafa zaman lafiya da gina kyakyawar dangantaka a tsakanin al’ummomi, mai tsayar da gaskiya ne, mai kishin al’umma da kwazo ne wanda ya bada gagarumar gudunmawa wajen kawo cigaba ba ga masarautar Toni ko jihar kawai ba, har ma da kasa baki daya”.
A cewarsa, “Da haka nake shawartar ‘yan Nijeriya da ke ruruta wutar furucin kalamun kiyayya da su daina maimakon haka, su zamanto ma su karfafa zaman lafiya a matsayin abin da kasa ke bukata”.