Al-Makura Ya Yi Kira Ga Al’ummar Ƙasa Da A Zauna Lafiya

Daga Zubairu T.M.Lawal lafia

Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Uamar tanko Al-Makura, ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su haɗa kai waje guda. Gwamnan ya yi wannan kira ne a sakon cika shekaru 57 da samun ‘yancin ƙasa. Takardar saƙon da ta fito ta hannun mai bai wa gwamna shawara a kar harkokin yaɗa labarai malam Ahmad Tukur, tana ƙunshe da jawaban gaisuwa da jaddada kira ga al’ummar ƙasa da su haɗa kai su zama tsintsiya maɗaurinki guda.

Gwamnan ya ce, “Ƙasarmu abin alfaharinmu ce, ga shit a cika shekara 57 da samun ‘yanci kai me za mu yi in banda godiyar Ubangiji, sanna mu haɗa kai mu zauna lafiya mu kuma bai wa gwamnatin Muhammad goyon bayan da take buƙata”.

Ya ƙara da cewa, kowa ya ga irin rawar da gwamnatin Buhari ke takawa wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa domin ci gabanmu, sannan kowane ɗan ƙasa ya kamata ya san rawar da zai taka wajen kawo ci gaban ƙasa a siyasar ƙasa.

Exit mobile version