Connect with us

Allah Daya Gari Bambam

Al’adar Kabilar Bakiga Ta Fi Son ‘Ya’yan Talaka Su Riga Na Masu Kudi Aure

Published

on

Filin namu na yau zai sada ku ne da mutanen kabilar Bakiga mazauna Kabale da kuma wasu sassa na gundumar Rukungiri. Sa’annan su ke zaune a Ndorwa, Rubanda,Rukigain kabale da kuma sassan kinkizi da Rubando na cikin Rukungiri sakamakon yawan su da ya haddasa musu hijira zuwa sauran sassa na kasar Uganda musamman kabarole, Rukungiri, kasese, Hoima, Masindi da Mubende sai kuma Rwampara, Ruhuma da Ibanda na Mbarara.  Har ila yau, sun zauna a masaka da Rakai. Mutane ne karfafa masu halittar karfi. Ma’abota yaren Rukiga na mutanen Bantu.

Asali

Babu wadda ya san takamaimai asalin Bakiga. Al’adu da dama sun kawo nasu ra’ayin wasu suka ce Mutanen na Bakiga asali suna rayuwa ne a Karagwe  lokacin hijirar su daga Bunyoro chan zamanin Luo. Ana kuma hada su da Banyambo na Tanzania, sai wata labarin kuma da ya fi wannan na farkon ma’ana suka ce asalin Bakiga na Buganza a Rwanda,hijira suka yi  daga Buganza dan neman kasar da za su yi noma mai albarka da kuma tsira daga fadace-fadace na cikin gida.

Daga Rwanda,an ce sun kara hijira zuwa Bwisa, zuwa Bugoyi daga nan kuma zuwa Rutchru,duk a Zaire,kafun daga bisani suka samu ma tsuguni a Kigezi, tunda su Bakiga na yaren Bantu ne wannan labarin zai iya zamowa gaskiya. Abun da ya zama gaskiyar shi ne su mutanen Bakiga suna cikin kabilar da ke yare da harshen bantu wadan da suka kaura daga Congo ta cikin Bunyoro, Karagwe, Rwanda da kuma zaire ta gabas kafun daga karshe suka zauna a kigezi.

Zamantakewa

Kabilar Bakiga sun kasu bisa zuri’zuria,mafi girmar zuri’a daga cikinsu shine, zuri’ar basiga,kabilar ta kunshi mutanen al’ummar da kuma shuwagabanninsu (omokuru w’omuryango). Basu yarda namiji ya auri mace wacce ta kasance ta fito daga cikin zuria’arsa ba.

Aure

Aure ya kasance al’ada mai matukar muhimmanci a tsakanin mutanen Bakiga. A gargajiyance babu wani aure da yake da daraja ba tare da an biya sadaki ba, ma’ana dukiyar aure. A wasu lokuta can baya iyaye ko kawunan miji kan iya hada aure a madadin yaronsu. Shiri na karshe yakan zo ne bayan an biya sadaki wanda yawanci yakan kasance uban ango shine zai bada. Wannan dukiya na aure yakan kunshi, Awaki da fartanya yawan kudin aure yakan danganta ne bisa matsayi matsayi, zuri’a da zuri’a, laifi ne mai girma kuma ya kasance babban abin kunya ne a ce an saida dabba bayan an bada ita a matsayin sadaki. Kabilar Bakiga kabila ne da suka kasance masu yawan aure-aure, yawan mataye yakan danganta ne daga matsayin yawan kasa (land)  da kuma yawan dukiyar aure(sadaki) bayan an biya sadakin yarinya sai kuma a rarraba wannnan dukiya tsakanin ‘yan’uwanta wadanda tafi kusanci dasu ,wadanda suka hada da Nyinarimi (kawu na wajen uwa)  da oshenkazi (goggo ta wajen uba). Idan kuwa har daya daga cikin wadannan mutane ya tafi cikin fushi ko rashin gamsuwa, toh a cewarsu zai iya yiwa ita wannan yarinya baki har ya kasance cewar ba za ta taba haihuwa ba ko kuma za ta fada laulayi mai matukar wahala da taimakon Allalolinsu abin bauta.

Maza sukan yi aure a kurarren lokaci ko a ce a lokacin da suka tara shekaru, wadannan tarin shekarun kuwa a cewarsu su ne tsakankanin shekara goma sha takwas da kuma ashirin, matayen kuma akan yi musu aure daga shekara goma sha hudu zuwa goma sha shida. Akwai wata dabi’a da suke da ita ta cewar abu mafi burgewa shi ne yaran da suka fito daga gidajen masu karamin karfi su ne ya kamata su rika aure da wuri kafin ‘ya’yan masu hannu da shuni, kafin aure kuwa yarinya za ta kasance ne a kebe a wani waje daban wanda a iya tsawon zamanta a keben zai kasancene ana bata abinci mai matukar kyau har ila yau kuma ana koya mata abubuwa da suka shafi zamanta kewar aure da kula da gida.

Advertisement

labarai