Al’adu Da Dabi’u: An Saki Reshe An Kama Ganye

Dabi'u

Kowace al’umma na da al’adu da dabi’unta wadanda ke bambanta ta da sauran al’umma da wadannan ne ta ke alfahari, su ne kuma abin dogaronta wajen kare mutuncinta da kuma kwarzanta kyawawan ayyukanta, don kyautata halayyar zamantakewar jama’anta da inganta al’amuransu da kuma habaka tattalin arzikinsu.

Wadannan dabi’u da al’adu su kan samo asali ne daga yanayin rayuwa da kuma wurin da al’umma ta kasance, suna kuma da nasaba da irin addinin da jama’an wannan al’umma ke bi. Dangane da haka babu wata al’umma da ke yarda al’adunta su gurbace ko kuma dabi’unta su karkata bisa tafarkin wata al’ummar can daban. Idan har haka ta faru a na iya cewa wannan al’ummar ta lalace kenan.

Al’ummar kasar Hausa ba su da al’adu ko dabi’un da suka wuce abubuwan da addinin musulunci ya koya masu da kuma sahihan dabi’un da suka gada tun kaka da kakanni, wadanda musulunci ya taras da su bisansu, bai kuma kyamace su ba, sannan kuma bai hana su aiki da su ba. Ke nan ana iya cewa al’ada aba ce da ta kunshi dukkan hanyoyin rayuwar al’umma tun daga kan yadda ake tafiyar da harkokin gudanar da gida ya zuwa dangantakar da ke tsakanin iyali da kuma fayyace hanyoyin yin mu’amala da juna da kuma tsara dokoki da hukunce-hukuncen da za su wanzar da zaman lafiya da lumana tsakanin al’umma.

Sai kuma dabi’un da al’ada ta haifar kamar su harshe da cinikayya da jana’iza da bukukuwa kamar na addini da na aure da haihuwa da nadin sarauta da murnar girbe amfanin gona da aikin gayya da kaciya da kuma yanayin tufafi da sutura sawa da kuma halayyar zaman gida da tarbiyyar yara da karantar da su da sauran su duk abubuwan da suka jibanci abinda dan Adam zai yi ko zai yi amfani da shi.

A Nijeriya akwai kabilu da muke da su sama da dari biyu da hamsin wadanda za a iya kasafta su cikin al’ummomi uku: Hausawa da Igbo da kuma kabilar Yarabawa, domin kamannu da dacewar wasu dabi’u da al’adu iri guda. Shi ya sa ko wata nahiya ce a kasar nan ya tafi da an kalle shi za a san daga al’ummar da ya fito, za a kuma girmama shi da yi masa karamci daidai da martabar al’ummar da ya fito daga cikinta. Za a iya gane shi ta hanyar sutura ko harshen sa ko kuma wata dabi’a ko al’ada da ya yi kokarin nunawa a wajen.

Amma sai dai a wannan zamanin dabi’u da al’adun Turawa sun samu gindin zama cikin al’ummomin nan guda uku har ma ta kai sun mamaye wasu daga cikin wadanda aka gada kaka da kakanni.

Ilimin Bokon da Turawa suka kawo mana ya taimaka ainun wajen wayar da al’ummar Hausa da kai, ya kuma kawo gagarumar cigaba irin ta zamani, amma kuma ya yi illa mai yawan gaske ga wasu kyawawan dabi’u da al’adun Hausawa.

Alal misali harshen Hausa ya yi rauni kwarai da gaske wajen ‘ya’yan Hausawan da suka yi ilimin Boko mai zurfi, domin kuwa da yawa daga cikinsu ba su iya yin cikakken bayani cikin harshen Hausa ba su gauraya da turanci ba. Wasu ma ba su san kalmomin Hausa da yawa ba. Akwai wadanda ma suna ganin yin magana ko jawabi a wajen gudanar da wani taro cikin harshen Hausa kauyanci ne da gidadanci, wasu kuma da gangar za su nuna maka ba su iya harshen da aka haife su a cikinsa ba. Mun sha ji da ganin ‘ya’yan manyan kasar nan suna tambayar wasu kananan kalmomi da suka kasa fahimtar ma’anonin su, ka duba abin kunya da takaici; amma kuwa idan aka juya wajen harshen Nasara ko Sarauniyar Ingila Elizabeth za ta sama masu lafiya. Kai ba ka ciyar da Adabinka gaba ba, ka tsaya kishin kayan aro kuma har kana tinkaho da shi.

Haka nan kuma ‘ya’yan Hausawa, maza da mata sun yi watsi da yanayin suturar da aka sansu da ita, mai mutunci da ke tabbatar da kamalarsu, sun rungumi dabi’ar sanya guntayen tufafin da ba su dace da tsarin addininsu ba wanda ya hana bayyana tsiraici ko nuna sigar ‘ya mace a fili.

’Yan matan Hausawa sun mance da gyalen rufe jiki, suna kyamar sanya hijabi wai don kada a yi masu dariya, a ce sun zama kidahumai. Su kuma ‘yan samarin sun daina sanya kaftani ko bunjuma da malum-malum, sun koma sanya wanduna masu yawan aljiffai da matsattsun wandunan da sai an yi dakyar ake kwabe su, ko kuma wadanda tsawonsu bai wuce kwaurinsu, su kakaba wata hula kamar sun kifa akushi, sa’annan su kwama wani irin gilashi da ya rufe masu rabin fuska. Wasu daga cikinsu ma sukan sanya takalma faska-faska kamar jirgin kwale-kwale. Idan ba ka san muhimmancin al’ada da kyawawan dabi’un malam Bahaushe ba me ya sa duk lokacin da ka tashi zuwa gidan surukan ka kake sanya kaftani? Ida ma ba ka da hula har ka je ka aro wajen abokai? To ko baby komai ka ga shigar suturar da al’adar Hausawa ta koyar da mu suna da kyau kuma suna tasiri a tsakanin al’ummar mu.

Ba matasa ne kadai ba suke rungumar wadannan tsatsibe-tsatsiben da suke cewa zamani ya zo da su, har ma da iyayensu, wadanda da gangan suke aikata abin da zai ba ‘ya’yansu damar kwaikwayonsu har ma su wuce gona da iri. Irin wannan al’amarin kuwa ya fi kamari ne a harkokin da suka shafi aure; tun daga nemansa har ya zuwa tarewa. An bi an sanya karya cikin al’amura bisa koyi da al’adun Yahudu da Nasara masu tsadar gaske, kuma ala-kulli-halin wai sai an yi kitson wance duk kuwa da cewa ba a da gashin wancen.

Idan an zo bikin tarewar amarya sai an sanya mata wata rigar da ba ta da tushe a musulunci, ta yaye rufin kanta don ta nuna gashin kanta ga jama’a yarbatsai, ba kyawun gani, don a ce wai ta hadu ta gwanance wajen kwaikwayon Nasara. A yanzu haka kowa na jin haushin al’adar da aka jajibo da rana tsaka ta yanka Kek din da ba shi a sunnar Ma’aiki, kuma ba shi cikin tsarin magabata. Babu kuma wanda zai ce ga yadda ranar uwa (Mother’s day) da kuma liyafar cin abincin dare a ranar tarewar amarya suka samo asali a dabi’un Hausawa, balle kuma rawar Owambe da Shoki da aka la’anci masu gantsarewa wajen juya mazaunai.

Ba ga nan kadai aka tsaya ba, iyaye suna ji suna gani za a kashe su da ransu, domin kuwa ‘ya’yansu ba su amsa sunayensu sai na kakanninsu, sa’annan kuma idan aka aurar da ‘ya sai ta bar sunan ubanta ta rarumo na surikinta, wato uban mijinta. An dawo daga rakiyar umarnin Mahalicci Allah da ya bukaci a kira kowa da sunan mahaifinsa ko da kuwa mahaifin ba musulmi ba ne. Alkunyar da aka san matasa da ita wajen neman aure yanzu ta kau. Ango da kansa yakan je zauren daura auren sa, amarya kuma da kanta ne za ta raba goron gayyatar bikin aurenta. Kai ni na ga amaryar da ta kira abokan ango bayan gama daurin aurenta da yamma, ta ce masu ita fa ta kosa a zo a dauketa a kai ta dakin mijinta.

Tunani da ayyukanmu sun koma daidai da na Majusawa ko Yahudawan da ke kyamar addininmu, ba su kuma kaunar ganinmu da kumbar susa. Ta haka ne mutuncin al’ummar Hausawa ya fara raguwa a idanun wasu al’ummomin kasar nan da ma na wasu kasashen, domin kuwa sun rigaya sun yi hannun riga da wasu kyawawan al’adunsu, sun rungumi na wasu can daban, wadanda ke kokarin kaskantar da al’adun su don ba su san mutuncinsu ba. Shi ya sa ake mayar da malam Bahaushe wani bican a wasu wurare, ake masa kallon kidahumi domin ya saki reshe ya kama ganye, ya bar al’adun da suka rufa masa mutunci, ya rungumi wadanda suke yaye masa mutuncin.

Ya dai kamata a sake tunani game da haka, a dauki kwararan matakan magance wannan mummunar matsalar ta aron al’adun wasu mu yafa, alhali kuwa su ba abin da ya dame su da namu, hasali ma kokari suke yi mu yi watsi da namu don mu zamanto ba mu ga addini, ba mu kuma ga adila, mun yi kamun gafiyar Baidu ke nan, ba mu ga tsuntsu ba mu ga tarko. An dai ce gadon gida alala ga raggo, kowa ya bar gida, gida ya bar shi.

Exit mobile version