Daga Munzir Yusif Ali
Allah kada ya kawo ranar yabo; haka Bahaushe ya ce. Kanawa sun tabbatar da wannan maganar in da a yau ido buɗe su ke nema da roƙon Alhaji Ibrahim Ali Al’amin Little ya zama jirgin fiton Talakawa ya tsamo su daga tasun da suka faɗa.
Kanawa mun gaji da tura mota ta na buɗe mu da hayaƙi, inda a yau talakawa mu ka haɗa kai muke da tabbacin Alhaji Ibrahim Ali Al Ameen Little ne mafitar Kanawa.
Mu na kira da babbar murya da ka fito ka amsa kiranmu ka zama ɗan takarar gwamnanmu a Jahar Kano saboda kyawawan halayensa da iya mu’amalarsa da taimakonsa da kishinsa ga Kanawa.
Mutum ne da ya ke jin ƙorafin jama’a a duk inda suka tare shi ba hantara ba ya guduwa Abuja ya bar jama’arsa. Kome na Alhaji Ibrahim ana samun rangwame don bai yarda da shan jinin talakawa ba.
Kano muna cikin wani yanayi marar musaltuwa inda muke kuka wiwi har wani ba ya rarrashin wani saboda halin ha’ula’i da muka tsinci kanmu wanda a ɓangarori mafi tsada a gun kowanne ɗan’adam.
Muhimmin ɓangare da a yau da muke ɗora hannu a ka shi ne Ɓangaren ilimi duk wanda ya kwana ya tashi a Kano ya ga yadda ɗan talaka ba shi da abin da Bature yake cewa Future kome an bar shi kara zube ba wani tartibiyar makoma. Malamai su ne tushen samar da kyakyawar makoma a duk inda ake neman karatu ingantacce. Hakan kuwa bay a tabbata sai an inganta shi kansa karatun malaman.
A yau malamai da dama an ɗora su ne don son zuciya ba wai don cancanta ba. Waɗanda kuma a ka ɗora, don cancanta an yi watsi da duk wani jindadi da walwala da promotion ɗinsu. Suna rayuwa ta hannu baka hannu kwarya ta yay a za a sami ingancin karatun? Ɓangaren muhallin da za a yi karatun shi ma ya zama tamkar kufai don haka daga ɗaliban har malaman ba me nutsuwa zuciyarsu cike da fargaba.
Duk wani fenti ba shi ne muhimmi ba wannan yaudara sunansa. Karatun yaranmu kullum ci baya a ke samu abin kunyar har ya kai ɗalibai na kammala firamare amma ba su iya ɗaura sunansu a takarda bakuma ba wanda ya damu saboda masu hannu da shuni da masu madafun iko duk yaransu na ƙasashen waje don haka ‘ya’yan talakawa ne a ciki.
Mun lura kullum Alhaji Ibrahim bakinsa akan ilimi yake yana da kishin yadda ɗan talaka yake a yau burinsa ya sauya alakalar karatun ɗan talaka shi ma ya zama kamar yadda ɗan masu hannu da shunin ya ke yi.
Bayan ɓangaren ilimi sai kuma harkar lafiya wanda shi ma jihar Kano ta zama koma ba asibitocin sannan a ma’aikatan jinyar sannan ba kayan aiki a asibitoci ba magani ba tsafta wannan abin ɓacin rai ne. Dogaro da kai yana cikin abinda ya zama barazana ga samari a yau Gawamnati ba ta samar musu da aiki ba sannan ba wani tsari da aka yi musu na yin sana’aoi.
Babban ƙudirin Alhaji Ibrahim Ali Al Ameen Little a inda duk yake shi ne yadda zai taimakawa waɗannan matsalolin namu shi ne burinsa don haka muke kira da shi ya zo ya cece mu don mun gwada da yawa amma da sun hau kujerar sai su manta da mu. Allah ya taimaki Kano da Kanawa Amin.
Daga Mai kishin jihar Kano, Kwamared Munzir Yusuf Ali,
Shugaban Little Youth Mobilization Forum 2019