Masana a fannin kiwon lafiya sun shawarci mutane masu fama da larurorin lafiya a kan kada su yi watsi da alamomin cutar yayin da suka fara bayyana a jikin su. Alamomin cutar hanta sun rabu kashi daban-daban daga kanana zuwa manya.
Almomin suna bayyana a jikin dan’adam bayan wata daya zuwa wata hudu da kamuwa da cutar. A wani lokacin kuma suna bayyana bayan mako biyu da kamuwa.
Da yawa daga cikin kwararrun lafiya da kuma likitoci sun yi gargadin cewa, alamomin ciwon hanta ba sa bayyana a kan jikin wadanda suka kamu da ita musamman kanana yara.
Jerin wasu alamomin na cutar hanta masu bayyana a jikin dan’adam.
1. Ciwon ko kuma kullewar cikin akai-akai.
2. Sauyawar launin fata zuwa doruwa.
3. Kadewar launin idanu zuwa doruwa.
4. Yawan jin kasala ko kuma gajiya tare da yanayi na zazzabi.
5. Kaikayi a wasu sassa na jiki.
6. Tashin zuciya da kuma amai.
7. Sauyawar launin fitsari da kuma bayan gida zuwa wani turarren launi da ba a saba gani ba.