Idris Aliyu Daudawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KIWON LAFIYA

Alamomin Ciwon Sanyin Mara Na Maza

by Idris Aliyu Daudawa
February 16, 2021
in KIWON LAFIYA
5 min read
Sanyin Mara
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ciwon sanyi wata cuta ce wadda tafi yaduwa ta hanyar jima’i saboda su kwayoyin halittun da suke sanya cutar ana yada sune daga wannan mutum zuwa wancan mutum, ta jini, maniyyi, ruwan farji ko ruwan jiki. Alamomin ciwon sanyi ga maza sun sha banban tsakanin mutane wadanda suka riga suka kamu da cutar.

Wannan kuma ya danganta ne da irin nau’in kwayar halittar cutar wacce ita ce take haddasa ciwon da kuma matakin da cutar ta takai a jikin mutum, wato wannan yana nufin, alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta dade da jimawa a jikin maras lafiyar.

samndaads

Haka nan kuma, su ma yanayin alamomin sun sha banban ta fuskar tsanani ko kuma saukin su, koda kumada akwai rashin ganin alama ko daya duk da cewar, ko akwai cutar a jikin marar lafiyar. Maza da yawa na zargin suna da ciwon sanyi ne kawai a lokacin da suka ga wasu alamomi da basu saba da gani ba (baki) ga al’aurarsu, misali , kamar: feshin kananan kuraje ko kaikayi, ko fitar da farin ruwa, jin radadin zafi daga maraina da dai sauransu. A takaice dai, alamomin ciwon sanyin maza za su iya buya amma gwaji a asibiti zai iya nuna akwai cutar idan da akwai ta.

Ciwon sanyi an fi yada shi ne ta hanyar jima’i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu dauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaduwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje. Haka kuma mutum zaya iya kamuwa da ciwon ta wasu hanyoyin na daban daba na jima’i ba.

Alamomin ciwon sanyin maza wanda aka fi samu bainar mutane (game gari):

  1. Kananan kuraje akan zakari, ko maraina ko kasansu.
  2. Kaikayi akan zakari (kan hular).
  3. Fitar da farin ruwa daga zakari, mai kalar madara ko dorawa, mai kauri ko wanda ya tsinke.
  4. Jin zafi lokacin yin fitsari.
  5. Jin zafi lokacin fitar maniyyi.
  6. Kuraje masu durar ruwa da fashewa akan zakari.

Alamomi ciwon sanyin maza wanda ba duk wanda ya kamu da ciwon bane yake ganin su:

  1. Rauni (gyambo) ga zakari ko maraina.
  2. Zafi da kumburin maraina
  3. Zafi da kumburi daga kwararo da fitsari da maniyyi suke fitowa daga cikin zakari.
  4. Zazzabi

1.Matsalolin jima’i da ciwon sanyi zai iya haddasa ma maza: Bincike ya nuna cewa cutar ciwon sanyi mai suna da turanci “Chlamydia” (kilamiidiya) zata iya sanya matsalar rashin karfin mazakuna idan ciwon yayi kamari ba’a magance shi ba. Cutar mabannaciya ce da take illa a boye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai dauke da cutar. Ana samunta bainar mutane da yawa. Rashin karfin mazakuta na nufin matsalar rashin cikakken karfin al’aurar namiji ko raguwar karfin al’aura yayinda aka fara saduwa ko kuma rashin mikewar al’aura lokacin da ake bukatar fara yin jima’i.

Bugu da kari, matsalar na iya zuwa da saurin kawowa/inzali. Rashin karfin maza zai iya saka magidanci cikin damuwa da tawayar jin dadin rayuwarsa ta jima’i, ko jin cewa bai cika mutum namiji ba, ko rashin haifuwa kasancewar ba zai iya yiwa iyalinsa ciki ba, saboda rashin mikewar al’aura. Zuwa asibiti da wuri ko cibiyar lafiya zai iya tsiratar da mai wannan matsala.

2 Rashin haihuwa:. Cutar sanyi mai suna “Gonorrhea” (Gonoriya) , kamar dai kwayar cutar “Chlamydia”, cuta ce daga halittar “bacteria” kuma zata iya labewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Duk da haka, tana zuwa da alamomi kamar fitar farin ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar, daga nan sai ya koma dorawa, mai kauri da yawa, wani lokacin harda dan jini-jini. Yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari, kaikayin dubura, zubar jini, murar makoshi/makogwaro, jan- ido ko kananan kuraje, ciwon gabobi da dai sauransu. Idan ba’a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sa rashin haihuwa ga namiji ko mace.

Nau’in ciwon sanyi (ire-irensu) suna da yawa kuma ko wanne iri akwai kwayar halittar dake haddasa ciwon da alamomin sa da kuma matakan cutar a jikin ‘dan Adam. Sunayen cututtukan da turanci suna da yawa kamar yawan cututtukan. Cutar sida/Kanjamau (AIDS/HIB) tana daga cikin manyan su saboda ita ma anfi yaduwa ta jima’i, kuma sau day awa ita ce ke gayyatar sauran cututtuka a jikin ‘dan Adam.

  1. Kankancewar Azzakari; Duk da dai cewa babu wani ingantaccen bayani a kimiyyance da yake nuna cewa ciwon sanyi yana sa azzakarin namiji baligi ya koma karami, akwai rahotanni da yawa daga mutane na korafin cewa sanyi ya sace masu girman zakari. Wannan zance haka yake a zahiri, masu ciwon sanyi sune suka fi lura da damuwa akan kankancewar alkalumman su.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima’i da kwayoyin halittu wadanda suke haddasa su (a yaren turanci):

SendShareTweetShare
Previous Post

Hasashen Masana Kan Alakar Sin Da Najeriya Shekaru 50 Masu Zuwa

Next Post

Real Madrid Ta Sake Samun Matsala

RelatedPosts

Cutar Kyanjamau Ko Sida

Cutar Kyanjamau Ko Sida

by Idris Aliyu Daudawa
18 hours ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa Su kwayoyin cutar sida (da Turanci...

Me Ke Kawo Karkacewar Baki Kwatsam?

Me Ke Kawo Karkacewar Baki Kwatsam?

by Idris Aliyu Daudawa
6 days ago
0

Daga Mustapha Wakili da Muhammad Zahraddin Shanyewar barin fuska larura...

Illolin Shan Ruwa Mai Sanyi Yau Da Gobe

Ruwa Da Amfaninsa A Jikin Dan Adam

by Idris Aliyu Daudawa
7 days ago
0

Amfanin ruwa guda tara a jikin dan Adam idan ya...

Next Post
real madrid

Real Madrid Ta Sake Samun Matsala

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version