Connect with us

LABARAI

Al’amura Sun Fara Inganta A Hukumar Inshorar Lafiya Ta kasa – Farfesa Muhammed

Published

on

An bayyana cewa, al’amura a Hukumar Lafiyar Inshorar ta Nijeriya sun fara inganta bayan tasgaro da rudanin da ta fuskanta a baya.

Babban Sakataren Hukumar, Farfesa Muhammed Nasiru Sambo, ne ya bayyana haka ranar Laraba a dakin taro na LEADERSHIP lokacin da ya ke yi wa shugabannin jaridar jawabi da ya kawo mu su ziyara ban-girma.
Ya ce, Hukumar Lafiyar Inshorar ta kasa a na iya cewar wata hukuma ce wadda tun lokacin da a ka fara maganar kirkiro ta, ta fara fuskantar matsala, wannan al’amarin kuma ya faro ne tun shekarar 1985 lokacin da Manjo Janar Buhari ne Shugaban Mulkin Soja, shi ne kuma wanda ya mika bukatar neman kafa ta.
Ya bayyana cewar sabanin yadda ya samu wurin lokacin da ya kama aiki a matsayin sa na Shugaban ta, inda rigingimu suka yi yawa, ga dai ta kungiyar ma’aikata, da su kuma ma’aikatan, har ma ya kasance a lokacin akwai bangare-bangare na su ma’aikatan da kowa ya na da nashi gwani. Har ma sai ta kai ga wani lokaci sai jami’an ‘yansanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wato tiya gas. Amma yanzu cikin ikon Allah al’amura sun koma yadda su ke.
Ta bangaren zaburar da ma’aikata domin su rika yin aiki kamar yadda ya dace da zamani wato aiki da komfuta, kamar dai yadda ya ce, “yanzu ma’aikata an fara koya masu yadda za su yi amfani da komfuta, wannan kuma abin ya kasance ne idan wadannan sun kammala sai kuma wasu”.
Dangane da yawan maganganu ko kuma korafin da mutane suke yi na yawan mutanen da suka yi rajista da Hukumar, yadda suke ta fadar saci- fadi, amma ya ce lokacin da ya zo a matsayin shugabanta mutane miliyan biyar ne suka yi rajista amma ya zuwa jiya Talata mutane miliyan goma ne suka yi rajista da ita. Ya kuma yi karin haske yadda wasu mutane mutane ke tsammanin Hukumar ta tarayya ce kawai, abinda kuma ya ce ba haka bane ba da akwai na jihohi ma suma suna da damar kafa tasu wanda kuma wasu jihohin sun kafa tasu.
Daga karshe ya nemi hadin kan kamafanin jaridar Leadership ya tallafa ma Hukumar wajen wayar da kan al’umma, domin su kara gane ayyukanta kamar yadda ya kata. Shi ma da yake na shi jawabin kafin a kammala shi taron na ziyarar ban girma Babban manajan darakta na kamfanin jaridar Leadership Mu’azu Elazeh ya bayyana cewar, kamfanin a shirye yake wajen taimakawa Hukumar, tunda yana da nau’in jaridu uku da suka hada da Leadership, Leadership Ayau da kuma National Economy, wadanda ya ce za su taimaka a kokarin da Hukumar take na kara wayar da kan al’umma dangane da ayyukanta.
Advertisement

labarai