Al’amura Tara Da Buhari Ya Hori Ministocinsa A Kai

Ministocinsa

Daga Yusuf Shuaibu,

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hori ministocinsa da manyan sakatarorinsu su kara zage damtse wajen gudanar da wasu manyan al’amura tara domin gwamnatinsa ta cimma burorinta na inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Shugaban ya bayar da wannan umurnin ne a wurin taron waiwayen ayyukan gwamnati na tsakiyar shekara da Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya ke yi, domin duba irin nasarorin da kowacce Ma’aikata da Hukumomi suka samar a cikin watanni shida na farkon shekara, inda ya bayyana cewa wajibi ne ministocin su mayar da hankali kan muhimman al’amura tara da gwamnatinsa ta sa a gaba.

Muhimman batutuwan sun hada da gina tubalin ci gaban kasar nan da dorewar tattalin arziki da inganta zamantakewa da rage radadin talauci ta hanyar fadada harkokin noma wajen samar da abinci da magance karancin wutar lantarki da man fetur.

Sauran sun hada da inganta harkokin sufuri da bunkasa sauran ababen more rayuwa da fadada harkokin kasuwanci ta hanyar kirkira da samarwa da inganta ilimi da inganta harkokin lafiya ga ‘yan Nijeriya.

Haka kuma gwamnatin ta dukufa wajen yaki da cin hanci da rashawa da samar da ingantacciyar gwamnati da kuma daukan matakai domin samar da tsaro mai dorewa.

Buhari ya bayyana cewa akwai bukatar samar da kyakkyawan alaka a tsakanin hukumomin gudanar da harkokin kudade domin bunkasa tattalin arziki.

A bayanin da ya fito daga bakin kakakinsa, Femi Adesina ya bayyana cewa shugaban kasa ya ja layi wajen bukatar samun damar kan abubuwan da gwamnatinsa ta mayar da hankali domin samun nasarori.

Domin cimma wadannan nasarori, Buhari ya umurci ofishin sakataran gwamnatin tarayya da ya fara shirya tarukan hadin gwiwa a duk wata uku a kan kowani muhimman batu bisa tsarin hadin kai. Ya ce manufar wannan taruka dai shi ne yadda za a aiwatar da dukkan wadannan muhimman batutuwa da bayyana matsaalolinsu da kuma magance su.

“Dole ne dukkan ministoci da sakatarorin dindindin su dunga halartar tarukan. Wannan ba taron da za a bayar da wakilci ba ne,” in ji shi.

Shugaban kasan ya bai wa ofishin sakataren gwamnatin tarayya umurnin hada hannu da karfe da masu ruwa da tsaki wajen gudanar da tsarin yadda ya kamata.

“Dole ne dukkan ministoci da sakatarorin dindindin su bayar da ba’asi kan ma’aikatunsu da rassan da ke karkashinsu game da kokarinsu kamar yadda aka tsara.”

Haka kuma, Buhari ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da wasu matakai wajen karin samun kudaden shiga na cikin gida da na ketare domin bunkasa tattalin arziki. Shugana Buhari ya yi alkawarin samar da ingantaccen ilimi da harkokin lafiya ga dukkan ‘yan Nijeriya.

A cewar shugaban kasan, ya umurci ma’aikatar jinkai da ta samar da wani tsari wanda zai bayar da kariya ga kudaden da ake kashewa kan zamantakewa. Ya kara da cewa za a sake bibiyan rawar da kananan kasuwanci suke takawa wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban kasa, inda gwamnati za ta yi dukkan maiyuwa wajen tallafa wa kananan kasuwanci.

A bangaren ababen more rayuwa kuma, shugaban kasa ya sha alwashin cewa gwamnatin tarayya za ta kashe kudade wajen tabbatar da ta kammala dukkan ayyukan samar da ababen more rayuwa kafin wa’adin gwamnatinsa ta shude.

Exit mobile version