Albashi Ma Fi Karanci:

Gamayyar kungiyoyin kwadago sun gabatar da sabbin bukatu na neman yin karin albashi mai tsoka ga ma’aikatan kasarnan, wanda zai dace da halin da tattalin arzikin kasarnan ke ciki a halin yanzu, ga kwamitocin nan uku na gwamnatin tarayya.

Babban Sakataren kungiyar kwadago ta kasa, NLC, Peter Ozo-Eson, ne ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai ranar Litinin a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, ya hakaito bukatar da kungiyar kwadagon ta gabatar shekaru biyu da suka shude na neman karancin albashi na 56,000, ga ma’aikatan kasannan.

Peter Ozo-Eson, ya ce, sun gabatar wa da kwamitocin uku bukatar sabon albashi ma fi karancin ne a zaman da suka yi da kwamitocin ranar 27 ga watan Maris 2018.

A cewar shi, tun kusan shekaru biyu kenan muka dauki matsaya, lokacin da muka gabatar wa da gwamnati bukatar na mu.

“Amma a lokacin da muka sami kiran da kwamitocin na gwamnatin tarayya suka yi na cewa duk wadanda abin ya shafa su gabatar da bukatun na su.

“A wajen amsawa bukatar na su, sai muka yi amfani da halin da tattalin arziki ke ciki wajen gabatar da sabbin bukatun na mu. Duk abin da muka gabatar ma su, mu ka kuma bukata daga gare su, sakamako ne na binciken da muka yi.

“Mun yi binciken ne ta hanyar amfani da halin da tattalin arzikin kasarnan ke ciki a yanzun, wanda hakan ya nu na mana wani abu na daban.

“Za mu tsaya ne kan abin da ke cikin takardar da muka gabatar wa Kwamitocin, wanda ba abu ne da ya kamata mu shelanta wa mutane ba,” in ji shi.

Ya kuma ce, sabbin bukatun na su na hadin gwiwa ne a tsakanin kungiyoyin kwadagon, NLC, da kungiyar leburorin ‘yan kasuwa, TUC.

“Mun rigaya mun gabatar ma su da sabbin bukatun na mu, mun kuma ba su duk hujjojin da muka dogara da su.

 

Exit mobile version