Abba Ibrahim Wada" />

Alex Iwobi Ya Jinjina Wa Arsenal Da Arsene Wenger

Alex Iwobi, Arsenal

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Alex Iwobi, kuma dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Eberton a yanzu, ya jinjinawa tsohon kociyan kungiyar, Arsene Wenger, bisa damar daya bashi a Arsenal shekaru 17 da suka gabata.

Iwobi dai ya koma kungiyar kwallon kafa ta Eberton ne daga Arsenal akan kudi fam miliyan 40 bayan ya shafe shekara da shekaru a Arsenal inda kuma ya buga wasanni 149 sannan ya zura kwallaye 15 ya kuma taimaka aka zura guda 23.

Dan wasan dai shine dan wasa na bakwai da Eberton ta saya bayan data dauki Jonas Lossl da Djibril Sidibe da Andre Gomes da Fabian Delph da Jean-Philippe Gbamin da kuma Moise Kean daga Juventus.

“Na taso tun ina karamin yaro da burin bugawa kungiyar Arsenal wasa kuma nasamu wannan dama har tsawon shekaru 17 ina tare da wannan babar kungiya wadda bazan taba mantawa da ita ba a rayuwa ta” in ji Iwobi

Ya cigaba da cewa “Akwai mutane da dama wadanda bazan taba mantawa dasu ba a wannan kungiya saboda irin taimakon da sukayi min na zama yadda nake a yanzu tun daga ranar dana fara zura kwallo ta farko a raga a filin wasa na Emirates da kuma ranar dana zura kwallo ta karshe a wasan karshe na kofin Europa a birnin Baku”

Ya kara da cewa ina mika godiya ta musamman ga tsohon mai koyarwa Mista Arsene Wenger bisa damar daya fara bani na nuna kaina a duniya sannan ina godiya ga magoya bayan kungiyar da ‘yan uwana ‘yan wasa da kuma mai koyarwa na yanzu Unai Emery bisa taimakona da sukayi.

Exit mobile version