Alex Telles Ya Ji Ciwo Tun Kafin Fara Firimiyar Ingila

Alex Telles

Mai tsaron bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Alex Telles ba zai fara buga wasannin kakar bana ba, sakamakon raunin da ya yi a makon jiya a lokacin atisayen kungiyar.

Telles mai shekara 28 a duniya, ba zai buga karawar Premier League da Manchester United za ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Leeds United da Southampton da kuma Wolberhampton ba.

Tun farko kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce dan wasan Brazil din zai yi jinyar makonni amma wasu gwaje-gwaje da likitoci suka yi, sai suka gane raunin mai muni ne.

Alex Telles shine ke maye gurbin dan wasan baya na Ingila, Luke Shaw idan ya samu matsala a kakar da ta kare, wanda ya yi wa Manchester United wasanni  23 a kakar wasan data gabata.

An yi ta alakanta shi da cewar zai koma buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Roma ko kuma Inter Milan a bana sai dai Manchester United ta bayyana cewa tana son ci gaba da rike dan wasan.

Exit mobile version