Alfanun Aure

BAƘON MALAMI Mufti Menk

Manzo (SAW) ya ce “in ku ka kiyaye harshenku da al’aurarku, Allah (SWT) zai amintar da ku ya sa ku a Aljanna”

Kowace halitta an halicce ta da abokiyar gwaminta, kamar rana da dare da namiji da mace,

Allah Ya halitta mana mata ne soboda mu ji daɗin juna da farantawa juna da kuma natsuwa da juna.

Kafin yin aure Shaiɗan na ƙawata kowanne jinsi sha’awa domin gaggauta yin aure ba tare da bin matakan shari’a ba, wanda ke kawo da-na-sani.

Allah (SWT) Ya sauƙaƙa hanyoyin yin aure ta yadda ba wani mahaluƙi da zai rasa hanyar yin aure, saboda da haka babu wani dalili da zai sa a ƙi yi har a faɗa tarkon Shaiɗan na yin zinace-zinace.

An azurta namiji da mallakar mace wadda zai kyautata mata a matsayin abokiyar zama.

Ya kamata iyaye su sani cewa ‘ya’yansu na iya zaɓar wanda za su aura matuƙar ba mutumin banza ba ne.

Ma’aurata na da ‘yancin zama su kaɗai ko kuma tare da wasu ma’autan amma, zama su kaɗai shi ya fi dace wa.

Allah (SWT) da Manzonsa su suka fi cancanta a yi wa biyayya fiye da kowa.

Manzon Allah na matuƙar sakin fuska ga matansa ta hanyar faranta musu rai.

Tattaunawa tsakanin ma’aurata na da matuƙar mahimmanci domin ta haka ne in akwai matsala za a iya warwarewa cikin sauƙi.

Idan ana son samun fahintar juna a cikin iyali ya kamata ya zama ana zaman tataunawa tare da kau da kai daga laifukan juna. A kwai buƙatar cikakkiyar amincewa da juna.

Wani abu mai mahimmanci shi ne, ma’aurata su kasance masu tausayawa junansu.

An buƙaci Manzon Allah (SWT) da ya kasance mai kyaykyawar hali wajen tafiyar da al’umma yadda za su yi masa kyakyawar fahinta, idan hori Manzo (SWT) ga yin haka ina ga mu tsakaninmu da matanmu?

Aure abu ne da ake buƙatar sadaukarwa domin gina zuri’a ta gari, a nuna yabawa ga duk abin da aka yi na kyautatawa juna.

Tsawa ga iyali na rage mutuncika kamar yadda tattausa murya ke ƙara mutunci.

Mafi kyawun wanda ya fi cancanta a aura shi ne wanda ke da tsoron Allah.

Haƙƙin mace na farko shi ne kula da bada tarbiya ga ‘ya’ya, sauran aikace- aikacen gida zata yi su ne a bisa kyautatawa.

Allah SWT yace “kada ku auri mushirikai”.

Bai kyautu ku auri wanda ke da kusanci ga iyayenku ko ‘ya’yanku ba.

Idan aka tashi zaɓar abokin aure a tabbatar da an zaɓi nagari, wanda ko wadda zai ko za ta taimaka wajen samar da zuri’a ta gari.

Abu ne mara kyau a hana yara aure matuƙar sun san haƙƙin yinsa, sai in akwai wani dalili na shari’a.

Baiko a Musulunci ƙulla yarjejeniyar yin aure ce tsakanin ma’aurata, idan an samu fahimtar juna, ba dole ba ne sai an yi taro ko an raba dema minti ko goro ba, wanna dukkaninsu al’ada ne, amma in ba haram ba ne ana iyayin su.

Mafi albarkar aure shi ne, wannda aka sauƙaƙa sadakinsa. Aure cikamakon imani ne. Idan kana ciyar da matarka da haramun, ba ka cika rabin imanin ba kenan kuma ba za a samu albarka cikin sa ba.

Haramun ne a gare mu mu halarci gurin tarurrukan da a ke aikata saɓo, koda kuwa ‘yan uwanmu ne suka shirya waɗannan taruka.

Babu kyau a kusanci mace lokacin watan azumi Ramadan don ka daɗaɗa mata. Haka ma lokacin aikin haji da kuma lokacin al’ada, a nan an yarda ku yi komai amma ban da saduwa. Allah ya umarce mu da tausaya wa matanmu. Idan sun ɓata maka rai wani lokacin za  su faranta maka.

Ya kamata maza su fahimci cewa, mata na bayar da gudummawa sosai wajen tarbiyyar iyali, saboda haka kada a nesantasu daga cikin iyali in ba da wani babban dalili ba. Ba za mu samu biyan buƙata ba matuƙar ba mu bi umarnin Allah ba. Annabi (SAW) ya ce, A kan samu bambanci tsakanin mutane 2 da ka raine su a gida daban-daban.

Saboda haka mu kasnce masu sauraro da kunnen basira, kada ya zamana ana hangen wani abu da ba za a iya yinsa ba.

Kada ka dinga bayyana sirrin tsakaninka da matarka.

Kada ka zama mai yawan musu, ka zama mai yin afuwa a kan waɗansu kura-kurai da aka yi maka.

Idan akwai matsala a faɗe ta yadda za a fahimci juna domin a samu bakin zaren warwarewa.

Duka haramun ne a Musulunci, ana kashe auren mace idan ana dukanta.

Abin da Alkurani mai girima ke cewa akan duka shi ne, irin dukan da ba zai cutar da ita ba  ta kowanne fanni. Idan an samu matsala tsakanin ma’aurata sai a samu waliyansu su shiga tsakani domin kawo sulhu, Alƙura’ani bai ce da zaran an samu matsala saki ce kawai hanyar maganin matsalar ba, maimakon haka za a yi ta menan hanyar magance matsalar ne, kuma lallai za a samu dacewa in dai har Allah a ke nufi.

Bai dace mita a kan bin da ya wuce ba, maa’urata su zama masu yafiya, su fuskanci gaba da fatan samun warakar matsalar da suke fuskanta, a rinƙa cizawa a na hurawa.

Ku aurar da ‘ya’yenku ga mazaje masu imani domin za su riƙe su cikin mutunci za kuma su faranta musu rai in kuma rabuwa ya zo za su turo su gida cikin mutunci.

Idan duk hanyoyin sulhu ya faskara, saki na iya zama mataki na ƙarshe, ba’a son furta kalmar saki cikin wasa, ya kamata ma’aurata su nemi ilimin yadda a ke saki tun kafin yin aure domin sanin mahimmanci da girman saki a addinin musulunci. An haramta wasa da abubuwa guda 3 saboda Allah ba Ya ɗaukansu a matsayin wasa, na ɗaya aure da saki da kuma ‘yantar da bawa.

Exit mobile version