Connect with us

LABARAI

Alfanun Bude Rassan Ofisoshin Fasfo Da Sansanonin Da Shugabancin Babandede Ya Yi A NIS

Published

on

Shugaban Hukumar shige da fice (NIS), CGI Muhammad Babandede MFR ya kawo sabon salon yin Fasfo a kananan ofisoshin hukumar da ke jihohi don kawo sauki ga matafiya da kuma rage wa hedikwatar hukumar nauyi don ta ji dadin fuskantar sauran ayyuka.

Wannan ya jawo an sami karin wurare da ake gudanar da aikin fasfo din. A farko dai an fara bunkasa karin wuraren fasfon ne inda a Abuja ya zama ana da shi a Hedikwata da Gwagwalada; akwai a Ikoyi, Alausa da Festac dake Legas; Kwaryar Kano da Dawakin-Kudu ta Jihar Kano; Babban Ofishin dake jihar Ogun, Abeoukuta da Sagamu; Babban Ofishin Jihar Delta Asaba da Warri; sannan akwai a kwaryar Jihar Oyo Ibadan, da kuma cikin garin Ibadan. Wasu manyan ayyuka ma suna kan hanya don ganin an inganta jin dadin masu yin fasfo.
Hukumar ta NIS karkashin jagorancin shugabanta Babandede tana kokari kullum don ganin ta In ganta ayyukanta, ta dakile duk wata nawa da ake samu, ta gyara ta shirya amsar takardar rokon aikin gaggawa, ta kuma shirya ganin ta cimma tsaruka irin na takwarorin na kasashen duniya.
Hukumar ta NIS ta sha alwashin ci gaba da bude sabbin ofisoshi don ganin ta cimma burinta na inganta jin dadin abokan kasuwancinta, akan doka da sharudan da aka gindaya Mata.

CIS Kunle Osisanya tare da Basarake Akarigbo na yankin Remo, Oba Babatunde Ajayi a fadarsa.

Yin fasfo yana tara mabukata fasfo din da yawa musamman a ofisoshin hukumar dake mafi kusa da mabukatan. Ta hakane hukumar taga yadace ta kirkiro sabbin ofisoshi a cikin manyan biranan kasa da kuma garuruwan dake da dimbin mutane aciki, don ganin an samu saukin cin koson jama’a, kuma hakan zai sa mabukatan su dinga zuwa sauran ofisoshin na Hukumara da ba’asan zuwa ganin nisantarsu da wajen zamansu, Kuma hukumar zata tabbatar an inganta jin dadin mabukata fasfo din.
Har ila yau dai, a wadannan kananan ofisoshin na jiha, wadanda suke da bukatar a basu wata dama kuma, kamar batar fasfo ko sacewa, ko gyara, ko neman izinin zama ‘yan kasa ga wadanda kundun tsarin mulki ya basu dama duk za su iya turawa hedikwata sannan a tura su inda yafi kusa da su don ganin an tabbatar da sahihancin maganar kuma an inganta jin dadinsu.
An kirikiri hanyar sadarwa ta zamani don ganin manema fasfo sun samu cikakken bayani game da neman fasfo din tsakaninsu da hukumar ba ta hanyar wasu maha’inta ba. Wannan ya dakile hanyar zamba da ake yiwa mafi yawancin masu neman fasfo.
Kwanturolan NIS na Ogun, CIS Kunle Osisanya, shugaba ne mai kyawun hali mai kwaikwayon kyawawan halin shugaban hukumar ta kasa CGI Muhammad Babandede MFR, inda a kodayaushe yake zama mai kokarin ya cika wadannan sauyi da shugaban hukumar ya kawo, kuma yana kokarin ya ga ya inganta jin dadin ma’aikatan hukumar, da kuma hada kai da sarakunan gargajiya don ganin sun taimaka masa wajen dakile hanyar shigowar bakin haure.
Advertisement

labarai