Alfanun Shagaltar Da Tubabbun Boko Haram Da Sana’o’i – Gwamnan Gombe  

Tubabbun

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bada shawarar cewa, ya kamata a kara karfafa gwiwar tubabbun ‘yan ta’addan Boko Haram da ake sauyawa tunani ta hanyar ba su horon sana’o’in hannu da za su shagaltar da su tare da dauke hankulansu daga sake daukar makamai.

Yana mai cewa, ta hakan za a samu raguwar matsalar tsaro tare da bai wa sauran wadanda ba su tuba ba damar ajiye makamansu domin tsarkake Nijeriya daga matsalolin tsaro.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa abin da ke faruwa a kasar Afghanistan da wasu kasashe, wani hannunka mai sanda ne ga hukumoni a Nijeriya su dauki matakan kandagarki don magance duk wani abin da ka je ya zo.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a matsayin babban bako, yayin wata tattaunawa kan sha’anin tsaro a kasar Afghanistan mai taken ‘darasin da ya kamata Nijeriya da sauran kasashen Afirka su dauka’, wadda kungiyar tsofin daliban kwalejin tsaro ta kasa suka shirya a Abuja, a cewar sanarwar da Isma’ila Uba Misilli, Daraktan yada Labarun Gwamnatin Jihar ya fitar.

 

Gwamnan wadda ya bayyana taron a matsayin abin da ya zo a kan gaba, ya ce Nijeriya da Afghanistan suna da abubuwa da dama iri daya, don haka abun da ke faruwa a can yana iya yin tasiri sosai ga Nijeriya da sauran kasashen Afirka.

 

Ya ce, abun da ke faruwa a kasar ta Afghanistan da wasu kasashe makamantan ta abun damuwa ne matuka, musamman ganin yadda matsalar tsaro ke barazana ga wanzuwar Nijeriya.

 

Ya kara da ce tun kafin ya zama Gwamna, ya kafa kwamitin harkar tsaro a jiharsa wadda aka daura wa alhakin bitar sha’anin tsaron da Jihar Gombe ke ciki da nufin samar da tsarin yadda za a bullowa lamarin a jihar.

 

Gwamnan ya ce ya kafa ma’aikatar kula da tsaron cikin gida da kyautata tarbiyya irinta ta farko tun lokacin da aka kirkirar jihar. Ya ce ma’aikatar tana shiga tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro da sarakuna da sauran kungiyoyin raya al’adu da nufin dabbakawa da cusa kyawawan dabi’un da ke tattare cikin al’ummarmu.

Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya (A tsakiya); Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro, Janar Lucky Irabor (daga dama) tare da Manjo Janar Mohammed Jibrin rtd, yayin wani taro kan sha’anin tsaro kwanan baya

Exit mobile version