Connect with us

RA'AYINMU

Alfanun Yakar Asarar Amfanin Gona Bayan Girbi

Published

on

Akalla Tan bilyan 1.3 ne na abincin da ake samarwa a wannan duniyar ke bacewa ko ya lalace a kowace shekara. Yawancin abincin da ake nomawa ba ya iya kaiwa ga fita daga kofar gonakin da aka noma shi, wanda hakan duk yana cikin abin da ke barazana ga samuwar wadataccen abinci. Wannan abincin da yake lalacewa ko bacewan, ya isa a ciyar da akalla mutane bilyan 1.6 a kowace shekara da shi. Wannan asarar abincin da ake yi, duk da cewa lamari ne da ya shafi duniya bakidayanta, amma dai ya fi kamari a nahiyarmu ta Afrika, wanda hakan ke yin illa ga wadatan abincinmu da kuma tattalin arzikinmu.

A yau, daya daga cikin kalubalen da ke fuskantar duniyar nan shi ne, ta yadda za a iya samar da abincin da dimbin al’umman da ke cikin duniyar wadanda kuma suke ta kara daduwa suke da bukata. A cewar hukumar abinci da harkar noma, ‘Food and Agriculture Organisation, FAO,’ tilas ne a kara yawan abincin da ake nomawa a duniyar nan da kashi 70, in har ana son wadata al’umman da ke cikin duniyar da abinci, al’ummar da aka kimanta za ta ta kai jimillan bilyan tara daga yanzun zuwa shekarar 2050. Amma tare da irin wannan dimbin asara da ake tafkawa bayan an girbe abincin a gonaki da wuraren ajiya a duk shekara, akwai tantaman ko za a iya samar da hakan.

Shekaru da yawa, kokarin ganin an habaka samar da abinci wata ka’ida ce ta kusan yawancin gwamnatoci. Amma abin bakin cikin shi ne, kimanin kashi 50 na ‘ya’yan itatuwa da ganyaye, kashi 40 na abinci mabunkusa kasa, da kuma kashi 20 na ire-iren su alkama, duk lalacewa suke yi kafin ma a kai su kasuwa. Mafi damuwan ma shi ne, kashi 70 na al’umman duniyar nan sun dogara ne ga harkan noman domin gudanar da rayuwar su, amma duk da hakan, rashin iya alkinta abincin yana ta kara wanzuwa a sashen Sahara na Afrika. Sannan kuma mafiya yawan al’umman sashen ba sa samun wadatan abin da za su ci wanda zai iya gina masu jiki. A gaskiya a namu ra’ayin, Nijeriya tana daya daga cikin kasashe 10 da suka fi rashin abinci mai gina jiki a wannan duniyar namu, tana kuma yin asarar kimanin Naira bilyan 10 a duk shekara ta hanyar abincin da ke lalacewa bayan an girbe shi, wanda wannan abinci ne mai yawan gaske.

Don haka, rage yawan abincin da ke lalacewa, zai kara wa kananan manoma milyan 470 yawan jarin su, wanda hakan ba karamin mataki ne na korar yunwa da talauci daga wannan duniyar ba. Kore sabubban lalacewar abincin, wata hanya ce ta kara yawan abinci mai sauki ba tare da sai an nemi kara yawan hanyoyin samar da abincin ba. Duk da cewa, ana yin asarar abincin ne a matakai daban-daban, a namu ra’ayin, akwai bukatar inganta hanyoyin hana asarar wanda masu bayar da gudummawa, gwamnatoci da masana ke yi. a lokacin da masana ke ta kokarin bullo da sabbin dubaru kan hakan, kananan manoma ba sa saurin fahimta da karban irin wadannan sabbin dubarun. In kuwa da za a yi aiki da wadannan sabbin dubarun a ko’ina, za su yi matukar taimaka wa wajen magance dimbin abincin da ake yin asarar na shi, ko kuma a rage yawan asarar daidai kima. Muna ganin ya zama tilas a canza wa mutane dabi’un su a kan hakan.

Kasancewar Nijeriya ma fi girman tattalin arziki a nahiyar Afrika tare kuma da bunkasar aiki a sashen na noma da suka hada da sabbin dubarun noman da ake samarwa, sarrafa shi da kuma hanyoyin raba shi, amma har yanzun dai akwai karancin hanyoyin hana yawan asarar da ake yi a wajen girbe abincin. Don haka, akwai matukar bukatar samar da hanyoyin adana abincin a cikin gaggawa a wannan sashen. Watau samar da yanayin da ya dace wanda zai rage yawan asarar da ake yi, musamman daga masana da masu bincike a sashen na noma na kasarnan.

Tabbatacce kuma gamsasshen tsarin yanayi zai taimaka sosai wajen rage asarar abinci, ya kuma taimaka wajen kyautata ingancin sa da yawan sa, kamar yanda zai taimaka wajen inganta shi yanda zai gina jiki ga masu cin sa. Misali a nan, rahoton hukumar da ke kula da adana abinci a yanayi mai kyau ta duniya, ya nu na Nijeriya tana da daya daga cikin mafi karancin hanyar adana abinci a Afrika na, 10,000m3, sa’ilin da kasashe irin su, Namibiya suke da, 150,000m3, Afrika ta kudu, 323,000m3, Morocco 1,700,000m3 da Misira mai, 3,250,000m3.

Ya zama mana dole mu kara kaimi, in har a matsayinmu na kasa muna son mu kyautata lafiya da tsaron abincinmu. Hakan kuma zai taimaka wajen rage yawan karancin abincin da ake fskanta, da tsadar abincin, ya kuma taimaka sosai wa tattalin arzikinmu, ta hanyar rage dogaro da shigowa da abincin daga wajen kasarnan. Rashin samar da tsaro a sashen abinci ba abin yarda ne ba, akwai kuma bukatar yin duk mai yiwuwa wajen kawar da hakan. Ya zama tilas masu ruwa da tsaki da kuma gwamnatoci su hada hannu su yi duk mai yiwuwa wajen magance hakan. Ta fahimtar hakan ne, muke yin kira ga kowa da a karbi wannan shiri na hukumar kiyaye lafiyar abincin ta duniya mai taken, SABE FOOD, ta hanyar hada hannu da kuma yin aiki a tare. Wannan mun tabbata, zai taimaka sosai wajen rage asarar abinci, ya kuma taimaka sosai wajen samar da wadatan abincin a duniya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: