Daga Ahmed Muh’d Danasabe,
Shahararren dan kasuwan nan dake garin Lokoja, babban birnin jihar Kogi, Alhaji Hamza Mai Goshi Taila, a ranan Asabar daya gabata, ya shirya kayataccen mauludin Annabi Muhammadu,tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a gidansa dake Unguwar Sarkin Noma dake birnin Lokoja.
Bikin mauludin, wanda dan kasuwan ya saba shiryawa kowace shekara, ya samu halartan manyan malamai da suka hada da Sheikh Yusuf Abdulkadir Zariya da babban limamin Unguwar Sarkin Noma, mallam Hassan Attah da Ustaz Ahmad Tijjani Sarkin Noma da Shugaban Zakirai na Lokoja, Mallam Abdulwahid Yabagi da babban limamin masallacin tudun natsira, Alhaji Abubakar Adamu da mallam Saidu Yusuf Abdullah Al-koji da kuma sauran al’ummar musulmi dake birnin na Lokoja.
Babban bako mai gabarar da lakca a wajen bikin mauludin, Sheikh Yusuf Abdulkadir Zariya, ya ce shirya mauludin Annabi, yana jaddada so da kuma nuna kauna ga manzon Allah( SAW), inda ya bayyana cewa duk wanda ya kashe dukiyarsa wajen jaddada kauna ga fiyayyen halitta, ba zai taba tabewa ba anan duniya da kuma can lahira.
Malamin addinin musuluncin wanda ya bada dogon tarihi game da rayuwar manzon Allah, ya kuma ce manzon Allah ( SAW) yayi fama da kafiran makka tare da fuskantar wahalhalu daban daban kafin kafuwar addinin Musulunci.
Sheikh Yusuf Zariya ya kuma kara da cewa duk wani dan Adam a duniya nan, albarkacin Annabi Muhammadu( SAW) yake ci, inda ya nanata cewa duk wanda ya dogara ga Annabi Muhammadu, baya tabewa duniya da lahira.
A karshe ya yabawa Alhaji Hamza Isah a bisa shirya mauludin, inda ya kuma yi masa addu’ar karuwar arziki da rayuwa mai albarka.
A nasa jawabin, wanda ya shirya mauludin, kuma sanannen dan kasuwan nan dake birnin Lokoja. Alhaji Hamza Isah Mai Goshi Taila, ya godewa Allah daya bashi lafiya da kuma ikon shirya mauludin Annabi Muhammadu daya saba shirya a kowace shekara, yana mai cewa soyayyan Manzon tsira( SAW) ne yake bashi kwarin gwiwar shirya mauludin Annabi, sannan ya kara da cewa komai ya samu a rayuwarsa na Annabi( SAW) ne.
Ya kuma godewa Sheikh Yusuf Abdulkadir Zariya, wanda yayi tattaki tunda daga birnin Zariyan jihar Kaduna har zuwa birnin Lokoja don amsa gayyatarsa da kuma gabatar da lakca.
Alhaji Hamza Isah har ila yau ya godewa sauran malamai da kuma al’ummar musulmi wadanda Allah ya baiwa ikon halartan bikin mauludin.
An dai gudanar da karatun Alkur’ani da addu’oi da kuma wakokin addinin musulunci wadanda Zakirai daban daban suka rera.