Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Alhaji Mohammed Abbas, Makama Karami Na Zazzau: Gwarzonmu Na Mako

by
2 years ago
in DAGA NA GABA
4 min read
Alhaji Mohammed Abbas, Makama Karami Na Zazzau: Gwarzonmu Na Mako
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

-Gogaggen ma’aikacin gwamnati

-mai sarauta

-Mai tallafa wa al’umma

Labarai Masu Nasaba

Ibrahim Gurso (1794-1814)

Hassan Sani Na Abba: Gwarzonmu Na Mako

 

Tarihinsa:

An haifi Alhaji Mohammed Abbas a Unguwar Fatika a cikin birnin Zariya ta jihar Kaduna a shekara ta 1957, kuma an sa ma sa sunan kawunsa ne wanda ya yi daidai da kyakkyawar al’adar al’ummar Arewa, na mafiya yawan sunan yaro, a kan duba sunan wani ne ko wata a cikin zuriyya a saw a yaron ko kuma yarinyar.Wanda aka sa ma sa sunansa shi ne marigayi Alhaji Abbas Usman, wanda ya taba zama Wakilin Doka, kafin rasuwarsa kuma aka nada shi Makaman Zazzau bisa kyakkyawar al’adar al’ummar Musulmi, musamman al’ummar arewacin Nijeriya, tun yaro na karami a kan sa shi a makarantar Allo, shi ma Alhaji Mohammed Abbas,ya ci wannan gajiyar da Allah ya ba shi damar samun ilimin addinin Musulunci tun daga rike Alloy a zuwa karatun litattafan addinin musulunci ma su yawan gaske.

Bayan ya kai shekarun zuwa makarantar firamare sai iyayensa su ka sa shi a makarantar firamare ta Tudun Wadan Zariya daga shekara ta 1964 a shekara ta 1968,saboda canjin aiki da aka yi wa mahaifinsa zuwa Kano, sai ya ci gaba da karatun firamare a makarantar firamare ta Gwammaj, daga shekara ta 1968 ya kammala karatun firamarensa a wannan makaranta a shekara ta 1970.

Kammala karatun firamarensa ke da wuya, sai ya sami shiga makarantar sakandare ta’ Bagauda Boys High School, ya yi karatu a wannan sakandare daga shekara ta 1971 zuwa 1975, bayan ya kammala sai kuma ya sami shiga kwalejin North East College Of Art Abd Science (NECAS), sai kuma ya sake samun damar karatu a Jami’ar Maiduguri daga 1977 zuwa shekara ta 1980, inda a wannan jami’a, ya sami takardar shaidar digiri kan kimiyyar siyasa daga wannan jami’a da aka ambata, bayan ya yi aikin yi wa kasa hidima a a garin Offa ta jihar Kwara.

 

Aikin Gwamnati:

Alhaji Mohammed Abbas , Makama Karami na Zazzau, ya fara aikin gwamnati a ma’aikatar kula da kananan hukumomi da kula da masarautu ta jihar Kaduna daga wata Satumba 1981 zuwa watan Disambar shekara ta 1982, ya na cikin aiki a karkashi gwamnatin jihar Kaduna, sai kuma ya yanke aikin ya koma aikin banki a watan Janairun Shekara ta 1983, inda ya sami aiki da bankin da ake kira Bank Of Credit And And Commerce International (BCCI) har zuwa shekara ta 1991, inda kuma ya sami canjin aiki zuwa hukumar kula da bunkasa yawon shakatawa ta Nijeriya, a matsayin babban jami’in mulki na wannan hukuma ta (NTDC), ya yi aiki a wannan hukuma har zuwa shekara ta 1993.

A shekara ta 1993 a lokacin da Cif Ernest Shonekan ya jagoranci gwamnatin rikon kwarya, a wannan lokaci ne aka kafa hukumar kula da kananan hukumomi sai cikin dan kanknin lokaci ya sami canjin aiki zuwa wannan ma’aikata, Alhaji Abbas ya kasance a wannan ma’aikata na tsawon shekara bakwai, wanda a hankali said a ya kai matsayin mataimakin darakta a bangaren mulki, amma a shekara ta 2000, sai aka yi ma sa canijn aiki zuwa ma’aikatar ayyuka da gidaje a matsayin babban sakataren bangaren bayar da kwangila na wannan hukuma, a dai wannan ma’aikata said a ya kai matsayin darakta, wanda ya ba shi damar sa ido na hanyoyi da dama a sassan Nijeriya.

Sai kuma a shekara ta 2003, sai aka yi ma sa canij naiki daga wannan ma’aikata zuwa ma’aikatar tsaro a matsayin mataimakin darakta, da aka dora ma sa aikin kula da duk mas’aloli da suka shafi hukumar sojojin sama, kuma a shekara ta 2006, sai aka kara ma sad a kula da duk wasu ayyuka da suka shafisojojin ruwa.

Wannan dama day a samu ya san abubuwa da dama da suka shafi wadannan bangarori biyu da aka ambata da kuma samun damar bayar da gudunmuwarsa, ciyar da wadannan wurare gaba A shekara ta 2009, sai kuma aka sake yi ma sa canijn aiki zuwa ma’aikatar lafiya ta gwamnatin tarayya a mukamin mataimakin darakta, mai kula da bangaren kasafi, ya kasance a wannan ma’aikata na tsawon shekara biyu da wata shida, amma a lokacin da aka yi ma sa karin girma zuwa babban darakta, sai aka kara yi ma sa canij aiki zuwa hukumar samar da wutar lantarki ta kasa, inda ya kasance a wannan hukumar har zuwa shekara ta 2011, ya zuwa lokacin da gwamnatin tarayya ta fara sayar da wasu kamfanoni.

Sauran ma’aikatun da Alhaji Mohammed Abbas ya yi aiki sun hada da canjin da aka yi ma sa zuwa ma’aikatar ilimi ta gwamnatin tarayya a matsayin babban darakta kan tsare-tsare da bincike da kuma kididdiga na wannan ma’aikata, a nan ma ya shafe wata uku ya na aiki a wannan ma’aikata ta ilimi, sai kuma aka sake yi ma sa canij aiki zuwa ma’aikatar sufurin jiragen sama,inda a nan ma ya yi wata uku a matsayin babban darakta a bangaren day a bari dagga inda ya taso.

Kazalika, a shekara 2013, ya sami canji zuwa hukumar kula da fanshon ‘yan sanda ta Nijeriya, inda ya bayar da gagarumin gudunmuwa, na gyara duk wata mtsala da ta shafi fanshon ‘yan sanda a Nijeriya baki daya, ya kasance a wannan hukumar har zuwa 18 ga watan Nuwambar shekara ta 2013, inda aka nada shi mukamin babbab sakataren dindindin a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya kasance a ma’aikatu daban-daban a gwamnatin tarayya, a ma’aikatun da su ka hada da hukumar kula da sufurin jiragen sama da ma’aikatar kula da tattalin arzikin kasa sai kuma ya yi babban sakatare a ma’aikatar Tama da Karafa daga Yulin shekara ta 2016 zuwa watan Disambar shekara ta 2017, wanda a wannan shekarar ce ya a je aikin gwamnatin tarayya a matsayin babban sakatare.

A ranar littinin 24 ga watan A gustan watan shekara ta 2020, Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris bisa amincewar gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’I ya nada shi Makama Karami na Zazzau, wanda ya ba shi damar kasancewa Makaman Zazzau na goma sha bakwai daga shekara ta 1804 zuwa 2020.

 

Kwamitocin Da Ya Yi Aiki A Cikinsu:

  1. Ya zama babban sakatare a hukumar bincike a hukumar man fetur ta kasa a karkashin fadar shugaban kasa.

2 Kwamitin hada bankin Federal Mortagage Bank, da kuma bankin bayar da rance, domin gina gidaje a karkashin ma’aikatar ayyuka ta tarayyar Nijeriya.

  1. Alhaji Mohammed Abbas, ya halarci kwasa-kwasai da dama a sassa daban-daban na kasashen duniya.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Tun Kafin Na Zama Marubuciya Na Ke Kaunar Marubuta – Mugirat Musa

Next Post

Kamfanonin Wutar Lantarki Sun Fara Aiwatar Da Sabin Tsarin Jadawalin Biyan Kudi

Labarai Masu Nasaba

Ibrahim Gurso (1794-1814)

Ibrahim Gurso (1794-1814)

by
12 months ago
0

...

Hassan Sani Na Abba: Gwarzonmu Na Mako

Hassan Sani Na Abba: Gwarzonmu Na Mako

by
1 year ago
0

...

Gwarzonmu Na Mako: Alhaji Nasiru Muhammad (2)

Gwarzonmu Na Mako: Alhaji Nasiru Muhammad (2)

by
1 year ago
0

...

Gwarzonmu Na Mako: Alhaji Umaru Ibrahim Battaiya

Gwarzonmu Na Mako: Alhaji Umaru Ibrahim Battaiya

by
1 year ago
0

...

Next Post
Gasa Tsakanin Ma’aikata Sinawa

Kamfanonin Wutar Lantarki Sun Fara Aiwatar Da Sabin Tsarin Jadawalin Biyan Kudi

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: