Masana sha’anin shari’a suna cewa, da a yi kuskuren hukunta mutum daya mai gaskiya, gara mutum dubu masu laifi su kubuta! Da yawan mutane sukan yanke wa ’yan finafinan Hausa hukunci bisa la’akari da danganta su da fasikanci da ake yi. Wannan ya sanya a mafi yawan lokuta mutane ba su cika tsayawa su nakalci ainihin abinda ya ke faruwa ba, kafin su soki ’yan fim ko su ki mara musu baya ba, alhali shi adalci ba ya la’akari da wanda ake takaddama akansa ba; yana dogara ne da hakikanin abinda ya afku wajen yanke hukunci.
To, amma a zahirin gaskiya ba kasafai ake bai wa ’yan fin irin wannan dama ta adalci ba. Da zarar an ce an kama dan fim bisa zargin ya aikata wani laifi, kai-tsaye sai wasu su shiga murna da farin ciki. Shi kuwa rashin adalci ka akan kafiri ne ba a yarda a yi shi ba. So ake a yi wa kowa adalci a rayuwa bisa la’akari da abinda ya aikata akan abinda ake magana akai.
Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano (KSCB) a karkashin jagorancin Isma’il Na’abba Afakallahu tana kama daraktocin Kannywood da wasu ‘crew’ na fim (wato ma’aikatan shirin fim wadanda ba jarumai ba ne) akan abubuwan da ake gani sun shafi hakkin fim, alhali ga furodusoshin fim din ba ta kama su, duk da cewa, sune suke da hakkin mallakar fim.
Bayyanannun misalai anan sune, hukumar ta tuhumi Darakta Sunusi Osca bisa zargin sakin waka ba tare da samun lasisi ba. Ta kuma tuhumi Mawaki Naziru Sarkin Waka shi ma bisa zargin sakin wata tsohuwar waka tun da dadewa a shekarun baya ba tare da shaidar izini ba. Sannan a kwanan nan ta tuhumi Darakta Mu’azzam Idi Yari da zargin fita daukar fim ba tare da takardar izini fita ba, duk da cewa yana da cikakkiyar rijista da hukumar.
Amma wannan bai hana Hukumar KSCB ta gurfanar da su a gaban kotu ba, kuma ga shi ba gurfanar da dukkan sauran ma’aikatan fim din a gaban kotun ba. Wato kamata ya yi a ce, idan KSCB tana son gurfanar da daraktan shirin ne, to dauke shi a matsayi na kamar dukkan sauran ma’aikatan shirin, in ya so su ma sai ta kai su gaban kotu, kamar yadda daraktan shirin yake a matsayin ma’aikaci. Haka kuma, ba a kama ko tuhumar furodusoshin ko kamfanonin ko kuma ‘yan kasuwar shirin ba.
Wannan matsaya ta Hukumar KSCB tana jefa ayoyin tambaya kan hujjojin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano na kai mutanen gaban kotu, inda hakan ya sa masu nazari sun kasa fahimtar mizanin da hukumar ke amfani da shi wajen tuhumar masu sana’ar shirin fim a Kano.
Har yanzu ba a ga an kai wani mutum da sunan ya karya doka ba matukar yana shiri da Babban Sakataren Hukumar, Afakallahu. Abin misali anan shine, Mawaki Sadik Zazzabi ya fuskanci tuhuma daga hukumar bisa zargin sakin wakar siyasa ba tare da izinin hukumar ba, alhali a fili take cewa, Mawaki Dauda Kahutu Rarara yana sakin wakokinsa ba tare da wata tsangwama ba. Shi kuwa Mawaki Zazzabi an kama shi ne a dalilin wata waka da ya yi wa babban dan adawar gwamnatin jihar Kano, a karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wato Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Zai yi wahala ka iya gane adalci a dalilan da za su sa a kama Zazzabi, amma a bar Rarara, idan ka kalli abin ta fuskar shari’a, ba siyasa ba.
Ba laifi ba ne, don an tafka siaysa a tsakanin ’yan siyasa kurum, amma shigo da kotuna a harkokin siyasa babban hatsari ne ga kasa bakidaya. Ya kamata a ce, idan ’yan siyasa sun shata dagar siyasarsu, su tsayar da abin iyaka siyasarsu, ba su rika jefa alakalai a ciki ba, su na yaudarar kotuna suna biyan bukatarsu.
Ba laifi ba ne, don gwamnati hana mukami ko wani rabon abu ga wanda ba ta tare da shi ba, amma kuskure ne babba ta rika amfani da kotuna wajen cimma irin wadannan bukatu na siyasa, domin kotuna waje ne da ake tsammanin duk wani dan kasa zai iya zuwa, don neman hakki ba tare da la’akari da imanin siyasarsa ba. Idan kuwa aka saba hakan, to za a jagwalgwala zamantakewar tarayyar kasar ta yadda duk wanda ya samu dama, zai iya yin amfani da ita yadda ya ga dama kuma ko ta halin kaka.
A zahirin gaskiya yana da kyau Gwamnatin Jihar Kano, musamman Gwamna Ganduje, ya tsoma baki wajen sanya mizanin da Hukumar Tace Finafinan jihar za ta rika amfani da shi wajen tuhumar masu sana’ar shirin fim, domin akwai zarge-zargen cewa, siyasa ko kuma wani ‘personal’ sabani da shugabannin hukumar na yanzu tsakaninsu da wadanda aka tuhuma din ne ke sanya akai su gaban kotu, musamman saboda kasancewar shi kansa shugaban hukumar na yanzu dan fim ne. Wato Afakallahu damo abokin guza kenan!
Tabbas abu ne mai kyau a rika hukunta masu aikata laifi, amma abu mafi kyau shine a rika hukunta wadanda suka dace da hukuncin kadai, domin adalci shi ke wanzar da nasara da zaman lafiya masu dorewa a koda yaushe a cikin al’umma!